Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Wasu ma’aikatan hukumar kwashe shara ta jihar kano sun koka bisa yadda aka rike musu Albashinsu har na tsahon harkimanin watanni shida .
Masu sharar da suka hadar da Mata da maza dattawa sun fito dauke da kwalaye dake dauke da rubutu dake nuni da neman gwamnan Kano ya kawo musu dauki saboda halin kakanikayi da suka shiga sakamakon rashin biyansu hakkokin nasu.
Jagoran masu zanga-zangar da ya buƙaci kadaura24 ta sakaye sunansa ya ce sun bi duk wata hanya da ta kamata domin su sami kudaden nasu amma hakan taki samuwa.

” An yi mana duk wata tantancewa da ta kamata, amma har yanzu hakkokinmu sun ki fito, Mun tuntubi MD REMASAB kuma yayi mana alkawarin tun kafin maulidi za a biya mu, amma hakan har yanzu bata samu”. Inji shi
“Muna kira gwamnan jihar kano ya tausaya yasa baki a biyamu hakkokinmu, saboda wallahi wasunmu sun fara fuskantar barazana daga wadanda suke binsu basussuka”. A cewar jagoran masu zanga-zangar.
Za mu tabbatar da umarnin gwamnan Kano na haramta bayar da filaye Barkatai – Kwamishinan Kasa
Kadaura24 ta tuntubi shugaban hukumar kwashe shara ta jihar kano Alhaji Ahmadu Haruna zago domin Jin ta bakinsa kan Zargin masu sharar, sai dai bai daga wayar da muka kirawo shi ba, kuma har lokacin hada wannan rahoton bai kirawo mu ba.
Inda masu sharak sukace du wani tsari da yakama ta subi sunbi domin ganin kudin nasu sun Isa garesu Amma haryanzu shurue
Masu Sharak da sukanemi a sakaya sunansu sunkara da cewa a safiyar wannan ranar suka Isa gidan gwamnatin kano domin Baiyanawa gwamnan korafinsu sai akaimusu gwamnan baya gari yana Abuja