Ƙotun ɗaukaka ƙara a Najeriya ta ce Alhaji Mustapha Haruna Jokolo ne sarkin Gwandu da ke Jihar Kebbi, saboda a cewarta ba a bi ƙa’ida ba wajen sauke shi daga sarautar da aka yi.
Alkalin kotun da ke zama a Sokoto Ibiowei Tobi, ya sake tabbatar da hukuncin da babbar kotun jihar Kebbi ta yi cewar gwamnatin jihar ta wancan lokaci ta saba ka’ida wajen matakan da ta ɗauka na sauke Sarkin Gwandu na 14 daga karagar mulki.
Saboda haka kotu ta yi watsi da ƙarar da gwamnatin jihar Kebbi ta gabatar a gaban ta, domin neman halarta matakan da ta bi wajen sauke sarkin.

Da wannan hukunci yanzu kallo ya koma kotun ƙoli wadda ake saran ta yanke hukunci na ƙarshe dangane da wannan shari’a, da aka kwashe sama da shekaru 20 ana tafkawa.
Ƙotun ɗaukaka ƙara a Najeriya ta ce Alhaji Mustapha Haruna Jokolo ne sarkin Gwandu da ke Jihar Kebbi, saboda a cewarta ba a bi ƙa’ida ba wajen sauke shi daga sarautar da aka yi.
RFI