Zaɓen kananan hukumomi: Gwamnatin Kano ta Sanya Dokar takaita zirga-zirga

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Gwamnatin Kano ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon sa’o’i 18 daga ƙarfe 12:00 na daren yau Juma’a zuwa 6:00 na yammacin gobe Asabar.

Gwamnatin ta ayyana dokar ce bayan tuntuɓar hukumomin tsaro kamar yadda wata sanarwa da Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin Gida, Baba Halilu Dantiye ya fitar a yammacin wannan Juma’ar.

Talla

Baba Dantiye ya buƙaci jama’a da su mutunta wannan doka ta taƙaita zirga-zirga domin bayar da haɗin kai wajen tabbatar da an gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar cikin aminci.

Ba fashi za mu gudanar da zaben kananan hukumomin Kano gobe Asabar. KANSIEC

Kwamishinan ya nanata ƙudirin gwamnatin na tabbatar da an gudanar da tsarkakken zaɓe na gaskiya da adalci.

Sanarwar da Kwamishinan ya fitar ta ƙara da cewa, dokar ta shafi dukkan ƙananan hukumomin jihar 44 da gundumomin zaɓe 484 da ke faɗin jihar.

Talla

Sanya dokar dai na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 24 gabanin zaɓen ƙananan hukumomin Kano da zai gudana a gobe Asabar, 26 ga watan Oktoba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...