Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya mikawa majalisar Dattawan Nigeria sunayen wadanda yake son nadawa a Ministoci.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a jiya laraba shugaban kasa Bola Tinubu ya sauke wasu daga cikin ministocinsa wasu kuma ya sauya musu ma’aikatun.

Shugaban majalisar Dattawan Godwill Akpabio ne ya bayyana sunayen mutanen da shugaban ƙasar ya tura musu.
Dambarwar Hisbah da Murja Kunya: Kotu ta yanke hukunci
Shugaban kasa Bola Tinubu ya turawa majalisar sunayen ne don ta tantance su kuma ta sahalle masa ya nada su a matsayin ministocinsa kuma yan majalisar zartarwa ta kasa.
Waɗanda aka kai sunayen nasu sun hadar da :

Dr. Nentawe yilwatda
Muhammadu maigari Dingyadi
Bianca ojukwu
Yusuf abdullahi Ata
Idi mukhtar maiha
Jumoke oduwole
Suwaiba Said Ahmad