Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Tsohon Dan takarar kujerar dan majalisar tarayya a yankin Danbatta da Makoda kuma jigo a jam’iyyar NNPP a yankin Dr. Sale Musa Wailare ya mika sakonsa na taya jagoran jam’iyyar NNPP na kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso murnar cika shekaru 68 a duniya.

” Babu shakka waɗannan shekaru 68 da jagoranmu yayi a duniya Shekaru ne masu matukar muhimmaci na gare shi kadai ba har da al’ummar jihar Kano da kasa baki daya, saboda irin aiyukan alkhairin da yayi da yadda ya bunkasa rayuwar ya’yan talakawa lokacin yana gwamanan Kano da kuma bayan ya sauka”.
Gwamna Abba ya taya Kwankwaso cika shekaru 68 a duniya
Dr. Sale Wailare ya bayyana hakan ne cikin wani Sakon da ya sanyawa hannu da Kansa kuma ya aikowa kadaura24.
Ya ce al’umma musamman masu karamin karfi ba zasu manta da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba , saboda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimta musu ta fuskoki daban-daban.

“A madadin ni kaina da Iyalaina da yan uwa da abokan siyasata dama al’ummar kananan hukumomin Danbatta da Makoda muna miko sakon taya jagoranmu murnar zagayowar ranar da aka haife shi, muna addu’ar Allah ya kara masa lafiya don ya ci gaba da taimakawa al’ummar jihar Kano da kasa baki daya”.