An sauke babban jami’in tsaron Shugaban Ƙasa Tinubu

Date:

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta janye Babban Jami’in Tsaron Shugaban Kasa Bola Tinubu, Adegboyega Fasasi daga Fadar Shugaban Kasa.

Daily Trust ta gano cewa DSS ta maye gurbin Fasasi da Rasheed Atanda Lawal, mai mukamin Mataimakin Darakta a hukumar, kuma tuni ya fara aiki a Fadar Shugaban Kasan.

Talla

Wasu majiyoyi a hukumar sun shaida mana cewa Fasasi wanda shi ne babban Jami’in Tsaron Shugaban Kasa tun da Tinubu ya hau mulki ya tafi kwas ne domin samun karin kwarewa.

Gwamna Abba ya taya Kwankwaso cika shekaru 68 a duniya

Majiyar ta ce Darakta-Janar na hukumar, Tosin Ajayi ne ya aike wa Tinubu takardar neman izinin tura Fasasi kwas din saboda muhimmancinsa.

Masu masaniya kan yanayin aikin DSS sun bayyana cewa maye gurbin Fasasi da hukumar ta yi bakon abu ba ne, suna masu bayyana cwea shi kansa ya kamata ya san da hakan domin abu ne da aka saba yi a hukumar.

Majiyar ta bayyana cewa kasancewar sabon shugaban hukumar ya fara aiki, akwai yiwuwar ya sauya wa wasu wuraren aiki musamman wadanda ke da kusanci da Shugaban Kasa.

Majiyar ta ce, “Tabbas na ji an maye gurbinsa da wani saboda an tura shi wani kwas. To ai wannan shi ne dalilin cire shi da muka sani.

Talla

“Irin wannan sauyin wurin aiki ba sabon abu ba ne a DSS musamman idan sabon Darakta-Janar ya fara aiki.

Talla

Aikinsu na sirri ne da binciken kwakwaf, saboda haka kowane shugaban hukumar zai so ya nada mutanen da ya fi aminta da su a muhimman wurare da Fadar Shugaban Kasa, kuma na farko shi ne Ofishin Babban Jami’in Tsaron Shugaban Kasa”, in ji majiyar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...