APC ce take kunna mana wutar rikicin cikin gida – NNPP

Date:

 

 

Jam’iyyar NNPP ta ce APC ce ke daukar nauyin rikicin da ke faruwa a wasu jam’iyyun adawa a kasar nan domin ta ci gaba da rike mulki bayan shekarar 2027.

Ajuji Ahmed, Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa ne ya bayyana hakan a taron kaddamar da yakin neman zaben dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar Ondo, Olugbenga Edema, da aka yi a Akure, ranar Alhamis.

Talla

Ahmed ya zargi APC da katsalandan cikin harkokin cikin gida na jam’iyyun adawa ta hanyar haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin mambobinsu don raunana tsarin jam’iyyun da kwace iko.

Rikicin NNPP: Gwamnan Kano ya Bijirewa Umarnin Kwankwaso, na cire wasu jami’an gwamnati

A cewarsa, wannan lamari da APC ke yi na zuwa ne yayin da shugabannin jam’iyyun adawa ke shirin gudanar da “tattaunawar hade kai” don kawar da jam’iyya mai mulki gabanin babban zabe.

“APC na yin duk abin da za ta iya don lashe babban zaben 2027. Tabbas, akwai shaidu a ko’ina cewa suna katsalandan cikin sauran jam’iyyun. “Amma abin ya rage ga sauran jam’iyyun siyasa su kare mutuncinsu kuma su tabbatar sun kasance guda ɗaya don kafa jam’iyyar adawa mai karfi da zata kawar da APC kafin da bayan zaben 2027,” in ji shugaban NNPP.

Talla

Ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ta shirya mika mulki bayan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, yana mai jaddada cewa NNPP tana tare da jam’iyyun adawa domin kafa kawance gabanin zaben 2027.

Talla

“Saboda haka, kofar mu a bude take ta yadda idan za a samu hadin gwiwa tsakanin dukkan jam’iyyun siyasa don shiga zabe, muna shirye don hakan,” in ji shugaban NNPP.

Daily Nigerian

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...