Maulidi: Nutsuwa wajibi ga duk masu Musulmi a yayin ambaton Manzon Allah- Malam Ibrahim Khalil

Date:

Da Abubakar Zaharadden

 

An bayyana Amana da nutsuwa a matsayin wasu daga cikin manyan abubuwan da suke tabbatar da ingancin taron Maulidi a fadin Duniya.

Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano Sheikh Mal. Ibrahim Khaleel ne ya bayyana hakan a daren jiya yayin wani taron Mauludin fiyayyen Halitta Manzo ( S.A.W ) da aka gudanar a garin Kano.

Talla

Wakikinmu Abubakar zaharadden, ya halarci taron Maulidin ga kuma karin bayani ta cikin rahoton daya hada mana.

A cewar Sheikh Malam Ibrahim Khaleel, Nutsuwa wata sifface da ta kamata a ce duk wani musulmi a duniya ya suturta kanshi da ita musamman a guraren da ake ambaton ALLAH da manzonsa, kamar taron Maulidi da masallatai da sauran guraren da ake daukaka kalmar ALLAH.

Gwamnan Kano ya bada tallafin Naira miliyan 100 ga wadanda gobarar kasuwar kantin kwari ta shafa

A cewar Malam Khaleel, dole ne duk wata halittar data kasance a tarukan Maulidi musamman ma Mutane dasu zama masu nutsuwa da tattara hankali guri guda domin jin yadda halitta da halayen Manzo ( S.A.W ) suke.

Koda yake zantawa da Manema Labarai a gefen taron Maulidin, Sheikh Khaleel yace wajibine mutane su zama masu nutsuwa a lokacin da ake zancen Addinin Musulunci.

Alhaji Mahmud Sa’id Adahama, daya ne daga cikin masu shirya tarukan kuma shi ne wanda ya shirya taron Maulidin na bana, ya kuma yi karin haske.

A taron Maulidin manya malaman Addinin Musulunci a Nigeria dama irinsu Mal. Nasidi Abubakar G/Dutse, Mal. Ibrahim me ashafa, da Prof. Umar Sani Fagge, da sauran Malamai ne suka gabatar da mukaloli akan fiyayyen hakitta Annabi Muhammad (S.A.W).

Talla

Halartar taruka irin haka dai na kara sanya nutsuwa da Il-hama a zukatan wadanda suka halarta kamar yadda Naseer Sa’id Adahama, daya daga ciki ya shaida mana.

Taron maulidin wanda shi ne karo na 17 da fara gudanarwa da kuma aka gudanar a Unguwar Nassara G.R.A dake Kano, ya kunshi manya da kananan malaman Addini musulunci da ‘yan kasuwa Yan’siyasa. da sauran al’umma na ciki da wajen Nigeria.

Kuma daga karshen an rufe taron da Addu’a tare da fatan samun zaman lapiya a jihar Kano dama kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...