NAWOJ a Kano ta nemi haɗin kan Gidan Radiyon Tarayya Pyramid don ciyar da kungiyar gaba

Date:

Kungiyar yan jaridu mata ta ƙasa reshen jihar kano NAWOJ ta bukaci hadin kan kafafen yada labaran dake Kano domin ciyar da harkokin kungiyar gaba.

Shugaban kungiyar NAWOJ ta jihar Kano Kwamaret Bahijja Malam Kabara ce ta bayyana hakan lokacin da ta ziyarci gidan Radio tarayya Pyramid Fm Kano.

Talla

“Mun Kawo muku wannan ziyarar ne domin yin godiya bisa gudunnawar da kuka bamu lokacin zaɓenmu har Allah yasa muka sami nasara, don haka Muna godiya Allah ya kara dankon zumunci “. Inji Bahijja Malam Kabara

Ta ce kungiyar ta na bukatar duk wasu shawarwari da suka dace wadanda zasu taimaka wajen ciyar da kungiyar gaba.

” Dama nan gidanmu ne don haka Muna bata za a bamu duk haɗin kan da ya dace, Sannan muna kira ga mambobinmu na wannan gida da ma sauran kafafen yada labarai da su rika halartar mitin idan an kirawo domin zuwansu yana da matukar muhimmaci”.

Da dumi-dumi: Jarumi Adam A Zango ya sami Mukami

Da yake nasa jawabin shugaban gidan Radio tarayya Pyramid Fm Malam Abba Bashir wanda shugaban sashin kula da ma’aikata na gidan Radio Umar Nuhu ya wakilta ya bada tabbacin gidan Radio zai baiwa kungiyar duk haɗin kan da ya dace domin kai wa ga gaci.

Ya Kuma shawarci sabbin shugabannin kungiyar da su sanya kungiyar a gaba su bijiro da abubunwan da za su kawowa kungiyar cigaba ta yadda za a yi alfahari da su ko da bayan sun kammala wa’adin su.

Talla

Kungiyar ta NAWOJ dai ta kai makamanciyar wannan ziyarar gidan Radio jihar kano da Guarantee Radio da Premier Radio da gidan talabijin na ARTV da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...