Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Gidan Talabijin na Qausain TV ya nada fitaccen jarumin fina-finan Kannywood kuma mawaki Adam A. Zango a matsayin Darakta Janar na gidan Talabijin.
Shugaban kamfanin Qausain, Alh Nasir Idris ne ya bayyana hakan, a wata sanarwa a ranar Litinin a Abuja, ya bayyana cewa nadin Mista Zango a matsayin Darakta Janar din ya fara aiki nan take.
A cewar sanarwar, an amince da nadin ne yayin wani taron hukumar daraktocin kamfanin.
Dalilai 2 da suka sa Gwamnatin Kwankwasiyya ta ce ta cire Sarki Aminu Bayero – Jafar Sani Bello
Alhaji Idris ya kara da cewa an nada tsohon Gwamnan Soja na Jihar Kano, Kanar Sani Bello (mai ritaya) a matsayin Shugaban Hukumar daraktocin kamfaninm
“Nadin Bello a matsayin Shugaban hukumar daraktocin kamfanin na tsawon shekaru hudu ne, kamar yadda dokar Kamfanoni ta tanada.

Idris ya ce an nada tsohon ministan sadarwa Farfesa Isa Pantami a matsayin mai sanya idanu kan harkokin shugabannin kamfanin.