Shahararren mawakin siyasar Nan Alhaji Dauda Kahutu Rarara ya jagoranci bude wasu makarantun Firamare guda uku da ya Gina da kuɗinsa a wasu kauyukan jihar Katsina.
Mawakin ya dai gina makarantar ne daya a Unguwar Da’iya Kahutu sai guda a Gidan Dari da kuma Barmi dukkanin su a karamar hukumar Dan ja dake jihar Katsina.
Da yake jawabi a wajen taron bude makarantun Alhaji Dauda Kahutu Rarara ya ce ba samar da makarantun ne saboda taimakawa al’ummar yankin da su sami nagartaccen Ilimi saboda shi ne gishirin Rayuwa al’umma.

” Na samar muku da wadanda makarantun ne da kudin aljihunna, don haka ina fatan iyayen yara za su nuna farin cikinsu ta hanyar tura yaransu makarantun tare da Kula da makarantun don su jima ana amfanarsu”. Inji Rarara
Da dumi-dumi: Jarumi Adam A Zango ya sami Mukami
A wata sanarwa da hadimin Rarara kan harkokin yada labarai Rabi’u Garba Gaya ya fitar, ya ce Rarara ya kuma dauki nauyin malaman makaranta 300 domin baiwa daliban ingantaccen Ilimi.
“Malaman za mu rabasu zuwa makarantun guda uku kuma za mu rika biyansu duk wata ka ga suma sun sami aikin yi, Sannan Muna kira a garesu da su zamu masu mai da hankali wajen yin aikin da aka dauke su”. A cewar Rarara

Alhaji Dauda Kahutu Rarara ya kuma ba da tabbacin zai cigaba da gudanar da aiyukan da zasu inganta rayuwar al’umma, don inganta rayuwar yara masu tasowa.