Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban kasa Bola Tinubu ya umurci babban sufeton yan sandan Nigeria, Kayode Egbetokun, da ya mayar da tsaro da tabbatar da zaman lafiya, da bin doka da oda a sakatariyar kananan hukumomin jihar Ribas.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa babban sufeton yan sandan Nigeria a jiya ya bayar da umarnin janye jami’ansa, daga dukkanin sakatariyar kananan hukumomin jihar Rivers.
Tinubu ya ba da wannan umarni ne a wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai ya fitar ranar Litinin.
A Musulunci Shugabanni ba su da rigar kariya – Sheikh Pantami
Ya ba umarnin ne domin dawo da zaman lafiya jihar, sakamakon yadda aka zargi yan daban tsohon gwamnan jihar Wike suka rika kona sakatariyoyin kananan hukumomin dake jihar.