Shan Ruwan Wata Rijiya Ya Yi Sanadiyar Rasuwar Mutane 7 a Kano Majalisar Kano

Date:

 

Majalisar dokokin jihar kano ta bukaci gwamnatin jiha ta kai daukin gaggawa garin Kanye dake karamar hukumar Kabo domin duba gidan ruwa da rijiyoyin garin.

Talla

Da yake gabatar da kudirin a yayin zaman majalissar na yau, dan majalissa mai wakiltar Karamar hukumar Kabo Alhaji Ayuba Labaran, ya ce ruwan wata rijiya da mutanen yankin suka sha ruwanta ya haifar da rasuwar mutane bakwai yayin da fiye da goma suke kwance a asibiti.

A Musulunci Shugabanni ba su da rigar kariya – Sheikh Pantami

Ya bukaci gwamnati ta tura masana domin gudanar da bincike akan musabbabin faruwar al’amarin.

Talla

Zaman majalissar wanda shugaban ta Alhaji Jibril Isma’il Falgore ya jagoran ta yayi kira ga gwamnati ta samar da ruwan sha mai tsafta ga al’ummar yankin domin kare afkuwar hakan anan gaba tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka mutu ya bawa wadanda suke kwance a asibiti lafia.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related