Dalilai 2 da suka sa Gwamnatin Kwankwasiyya ta ce ta cire Sarki Aminu Bayero – Jafar Sani Bello

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Tsohon Dan takarar kujerun gwamnan jihar Kano Alhaji Jafar Sani Bello ya bayyana wasu dalilai guda biyu da yace su ne suka sa gwamnatin jihar Kano ta ce ta cire Sarkin kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero daga gadon sarautar Kano.

” Kowa ya ji lokacin da Kwankwaso ya fito ya ce basu da matsala da sarkin Kano Aminu Ado, ya kuma ce mutumin kirki ne to in har haka ne don me za ku zalince shi ko don ya gaji mahaifinsa ?” .

Talla

Jafar Sani Bello ya bayyana hakan ne yayin wani taron neman labarai, wanda da ya gudanar a jihar kano ranar Litinin, domin mayar da martani ga kalaman Tsohon gwamnan jihar kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Ya ce dalili na farko da yasa Kwankwaso yasa aka cire Sarkin kano na 15 shi ne saboda Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero bai goyi bayansa ba a zaɓen Shekarar 2003, wanda hakan tasa bai samu yayi tazarce ba.

Rikicin Rivers: Tinubu ya baiwa IGP umarni

” Na biyu kuma shi ne ya taba cewa me yasa za a yanke karamar hukumar Madobi daga masarautar kano a kaita Karaye, bayan daga kan gadar madobi har zuwa gidan sarkin Kano bai wuce tafiyar mintina 20 ba” a cewar Jafar Sani Bello

Jafar Sani Bello ya ce waɗannan ne kawai dalilan da suka sanya gwamnatin jihar Kano ta ce ta cire Sarki Aminu Ado Bayero daga gadon sarautar, amma ba don ya yi musu komai ba domin shi ma Kwankwaso ya fadi cewa “mutumin kirki ne ba su da matsala da shi”.

Ya ce a lokuta daban-daban Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi kalamai masu cin karo da juna akan wannan batun.

Talla

” A Wata hira da yayi da BBC Hausa bayan cewa an cire Sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero, Kwankwaso ya ce bai da labari amma zai zo Kano ya binciki yadda akai hakan, kwatsam kuma sai ga buryarsa tana yawo wacce ya ke ba da umarnin yadda za a cire Sarki, yanzu kuma ya zo yana cewa ba Sarkin Mutumin kirki ne ba su da matsala da shi”. Inji Jafar Sani Bello

Ya ce Kwankwaso shi ne kanwa uwar gami kan duk abubunwan da suka faru a jihar kano musamman kan batutuwan da suka shafi masarautar Kano da suka ce sun cire Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, sun kawo wanda aka cire shi saboda laifukan da ya aikata kuma ya kasa Kalubalantar laifukan da aka ce ya yin a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...