Sufeto-Janar na ƴan sanda ya bada umarnin janye jami’an ƴan sanda da su ka mamaye sakatariyar ƙananan hukumomi a Rivers na tsawon watanni uku.

An mamaye sakatariyar ne a watan Yuni sakamakon rashin jituwar da aka samu tsakanin shugabannin kwamitin riko da ke goyon bayan Gwamna Siminalayi Fubara da kuma shugabannin kananan hukumomi da suka sauka, wadanda suka kasance masu biyayya ga Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT).

Daily Trust ta rawaito cewa sai dai a yau Litinin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansanda a jihar Rivers, SP Grace Iringe-Koko, ya ce sabon kwamishinan yansandan jihar, CP Bala Mustapha, ya mika umarnin babban sufeton ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun. domin a janye dukkan jami’an da aka tura a baya don rufe sakatariyar da kuma tsare ta.
Ya ce umarnin janye ƴansandan na nan take ne.