Sarki Aminu Bayero ya kai ziyarar ganin asarar da aka tafka a gobar Kantin Kwari

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado ya kai ziyarar jajantawa Yan kasuwar Kantin Jim kadan da dawowarsa daga ziyarar aiki da ya je Abuja.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran sarkin Abubakar Balarabe kofar Na’isa ya aikowa kadaura24, ya ce dubun dubatar masoya da magoya baya ne suka yi cincirundo domin raka mai Martaba Sarkin kasuwar ta Kantin kwari.

Talla

Da yake jajantawa wadanda suka gamu da ibtila’in gobarar, Sakin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi addu’ar Allah ya mayar da asarar da akayi a kasuwar tareda addu’ar Allah ya kiyaye afkuwar hakan anan gaba.

A 2027 za mu sallami Kwankwaso daga Siyasa – Doguwa

Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma godewa Jami’an Hukumar kashe gobara ta jihar Kano da Jami’an tsaro da Kungiyar Yan kasuwar da dai daikun al’uma bisa yadda suka bada dugunmawa wajan tabbatar da kashe gobarar.

Sarkin daga nan sai ya bukaci Yan kasuwa da sauran al’umma su cigaba da yin Addu’o’i domin kiyayewar afkuwar irin wannan ibtila’i tare da neman samun sassaucin al’amura na rayuwar yau da kullum.

Talla

Mai Martaba Sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai ziyarar aiki ne babban Birnin Tarayya Abuja tare da halartar wasu tarurruka, inda daga dawowar sa ne ya zarce domin yin jaje ga Yan kasuwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...

Rundunar Sojin Amuruka ta kammala tsara yadda za ta kawo wa Nigeria hari

  Rundunar sojin Amurka da ke Afirka, AFRICOM, ta gabatar...

Kalaman Trump: Gwamnatin Nigeria ta Fara tattaunawa da Gwamnatin Amuruka

Gwamnatin Najeriya ta ce a gwamnantance tana tattaunawa da...

Ba zan bar Siyasa ba har lokacin da zan bar Duniya – Mal Shekarau

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce...