Yancin kai: Muhimman bangarori 6 na jawabin shugaban ƙasa Bola Tinubu

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

A ranar talatar nan ne Nigeria ta cika shekaru 64 da samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka na burtaniya.

A duk irin wannan rana shugaban ƙasa ya kan fito ya yiwa al’ummar kasa jawabi, ya yaba masu bisa kokarinsu na kasancewa kasa daya al’umma daya, Sannan ya bayyana nasarorin da ya samu da kuma taya su murnar zagayowar wannan rana.

Kamar kowacce shekara a yau ma shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya gabatar da jawabin ga yan Nigeria kamar yadda aka sanar tun ajiya.

Talla

Ga wasu muhimman bangarori daga cikin jawabin shugaban ƙasar da Kadaura24 ta saurara.

Tsaro:

Jawabin shugaban ƙasar ya tabo matsalolin tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar musamman Arewa maso gabas da arewa maso yamma, Inda ya ce gwamnatinsa tana ita bakin kokarinsu ta wajen magance matsalolin don tabbatar da zaman lafiya ga yan Nigeria.

Ya ce a cikin shekara guda gwamnatinsa ta kawar da kwamandojin Boko Haram sama da 300 tare da hallaka shugabannin yan fashin daji masu tari yawa wadanda suka addabi al’umma.

Ya ce sojojin ƙasar suna aiki ba dare ba rana domin kawar da duk wani nau’i na ta’addanci a cikin al’umma.

Tattalin arziki:

Abu na biyu shi ne ya ce gwamnatinsa tana iya bakin kokarinta wajen inganta tattalin arzikin Nigeria daga mawuyacin halin da yake ciki.

Ya ce ya fito da manufofin sauya fasalin tattalin arzikin kasa wanda ya jawo al’umma suke kokawa da shi, amma dai ya ce hakan ba ba dan lokaci ne domin zuwa yanzu an fara ganin cigaba Kan aiyukan garanbawul din da ake yiwa tattalin arzikin.

Ya ce yanzu haka saboda ci gaban tattalin arzikin da ake samu masu zuba jari daga kasashen waje a shekara guda sun zuba jarin Dala biliyan $30 a fadin Nigeriya.

” Tsarin da babban bankin Nigeria CBN ya dauka na kiyaye manufofin Kudade ya tabbatar da tsaro da tabbas a kasuwar chanjin kudaden waje.

Ya ce ya gaji Dala biliyan 33 a asusun ajiyar Nigeria na kasashen waje, sannan sun biya bashin dala biliyan 7 da biyan sauran basussuka da ake bin Nigeriya kamar yadda suka yi alkawari.

Ya ce duk a kokarinsa na ganin an inganta walwalar Nigeriya ne tasa gwamnatinsa ta dawo da yancin cin gashin kan kananan hukumomi a Nigeriya ta fuskar kudade.

Talla

Kayan Abinchi:

Ya ce yasan ana fama da matsalolin tsadar kayan abinchi, amma ya ce ba a Nigeriya ne kadai aka fuskantar wannan matsala ba , amma ya ce gwamnatinsa tana iya bakin kokarinta domin wadata kasar da Abinchi.

Ya ce gwamnatinsa tana bunkasa harkokin Noma ta hanyar bada tallafi ga manoma da samar da takin zamani ga manoma don su sami sauki wajen gudanar da aikin nasu na noma don wadata kasar da Abinchi.

Ya ce sun samar da ma’aikatar kera kayan noma na zamani wadanda zasu taimakawa manoman wajen barin tsahon tsarin noma zuwa sabon tsarin noma wanda zai taimakawa ƙasar.

Sufuri :

Game da batun sufuri, shugaban Bola Tinubu ya ce suna daukar matakan da suka dace domin saukaka al’amuran sufuri a tarayyar Nigeria.

Ya ce a kokarin hakan ne suka fara bayar da da motoci masu amfani da Iskar Gas da masu amfani da lantarki ga kungiyoyin Kwadago da na dalibai domin saukaka ma’aikata da dalibai a Nigeriya.

Shugaba Tinubu ya kara da cewa gwamnatin tarayya a shirye take ta taimakawa gwamnonin jihohin Nigeria don su sayi motocin masu amfani da Iskar Gas don saukakawa al’ummarsu harkokin sufuri.

Talla

Matasa:

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta fito da damamaki masu yawa ga matasa domin tallafa musu kasancewar suna kashin bayan cigaba kowacce al’umma.

Ya kuma sanar da cewa za a gudanar da wani gagarumin taron matasa na kasa wanda zai kunshi dukkanin matasa daga bangarorin kasar nan, kuma yace taron zai baiwa matasa bayyana Kalubalensu da kuma hanyoyin da za a magance su, Sannan ya bayar da tabbas gwamnatinsa zata aiwatar da shawarwarin da aka bata bayan taron.

Sanna ya yi alkawarin cigaba da baiwa matasa damar shiga harkokin gwamnatinsa ta yadda matasan zasu fahimci abubunwan da Ake yi a gwamnati ko dan gobe.

Sannan ya yi alkawarin gwamnatinsa ta karkashin ma’aikatar Kwadago da samar da aiyukan yi, za ta samar da aiyukan yi ga matasa miliyan biyu da rabi a kowacce shekara don rage adadin matasan da ke zaman kashe wando.

Hadin kai

Shugaban ƙasar Nigeriya Bola Ahmad Tinubu ya kuma bukaci al’ummar kasar da su zamo masu haɗin kai, inda yace da shi ne kasar zata kai duk Inda Ake bata.

Ya bukaci kowa ya ajiye bambancin kabila ko addini ya bayar da gudunmawa wajen ciyar da ƙasar gaba don yan baya su amfani kasar kamar yadda gwamnatinsa take fata.

Daga ƙarshe dai ya yabawa Yan ƙasar bisa juriyar da suke nunawa a wannan lokaci mai matukar kalubale, inda ya bada tabbatacin nan gaba kadan komai zai daidaita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Bam ya fashe a Kano ya hallaka wasu ya kuma jikkata wasu

Aƙalla mutum biyar ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin...

Kotu a Kano ta sami wani Tela da laifin takurawa makwabtansa da karar keken dinki

Wata kotu a Kano ta samu wani tela da...

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...