Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai yiwa al’ummar Nigeria jawabi da safiyar ranar Talata 1 ga watan Oktoba da karfe 7 na safe.
A sanarwar da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayi Onanuga ya fitar, ya ce jawabin na shugaban kasa wani bangare ne na bikin tunawa da ranar ‘yanci karo na 64.

Sanarwar ta kara da cewa za a sanya jawabin shugaban ƙasar a gidan Talabijin na ƙasa NTA da gidajen Radio Nigeriya, don haka ake umartar sauran kafafen yada labarai da su za jonawa da su domin yada jawabin shugaban ƙasar.
