Nijeriya na shirin hawa tsarin kama-karya na jam’iyya guda – Atiku Abubakar

Date:

 

 

A yayin da Nijeriya ke bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi kira ga manyan ‘yan siyasa su hada kansu don kare dimokuradiyyar kasar daga hawa kan tsarin kama karya.

Atiku, a wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kansa, ya ambato cewa fannin siyasa na samun cikas a sannu a hankali a kasar nan a yayin da jam’iyyun adawa ke kara samun rauni a daidai lokacin da jam’iyya mai mulki ke haddasa wutar rikici a jam’iyyun don hana su tasiri.

Dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, ya koka kan cewa Nijeriya na neman zama mai bin tsarin jam’iyya daya na kama karya, ya yi kira ga ‘yan siyasa da dattijan kasa da su tashi tsaye wajen ceto dimokuradiyya.

Jagoran ‘yan adawar ya ce, “A yayin da dimokaradiyya ke zama ado ga bangarorin mu a bisa matakan bin doka da Oda, har yanzu ba mu kai matakin ci gaba ba na rainon tsarin siyasar bai wa kowa dama a dama da shi da kuma tabbatar da zabe na gaskiya”.

’Yan Sanda Sun Gargaɗi Masu Shirin Yin Zanga-Zanga A Kano

A don haka, yayi kira ga jiga jigan siyasa da su hada kai wajen kare dimokuradiyya daga kama karya.

Talla

“‘Yan mazan jiya sun hade kai kan buri guda, sun bada muhimmanci ga samun ‘yan cin gashin kan mu ta hanyar gwagwarmaya cikin lumana. Abin da muke murna a yau shi ne alkhairin da hadin kansu ya samu da al’umomin da suka biyo bayan su, ” inji Atiku.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar, ya kuma taya ‘yan Nijeriya murna na cika shekaru 64 da samun ‘yanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...