Kamfanin Gerawa ya dauki nauyin wasan kallon kafa tsakanin bankuna a Kano

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

A kokarinsa na ganin ya kara kyautata Alakarsa da al’umma, Kamfanin Shinkafa na Gerawa Rice Mills ya dauki nauyin shirya wasan sada zumunta tsakanin bankuna dake fadin jihar kano .

Da yake bude wasan a filin wasa na Kano Pillers dake unguwar sabon gari a Kano, Shugaban rukunonin kamfanin GMD Alhaji Dr. Ibrahim Muhammad Gerawa ya ce sun dauki nauyin Wasan ne domin kara kyautata Alaka tsakanin kamfanin da kamfanonin yan uwansa don cigaban jihar kano.

Talla

” Babu shakka wannan rana ce mai matukar muhimmaci a wajen mu, saboda yadda muka dauki wannan wasanni na sada zumunci, wanda hakan zai inganta Alakar dake tsakanin kamfanonin da bankuna a jihar Kano, Sannan kuma hakan zai ba da damar sanin juna wanda hakan zai matukar taimaka mana ko da a zamantakewarmu”. Inji Alhaji Ibrahim Muhammad Gerawa

Ya ce wasanni irin waɗannan suka taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma, Sannan kuma zai ba da dama ga ma’aikata su motsa jikinsu kuma su kara samun lafiya, kamar yadda masana kiwon lafiya suke cewa motsa jiki na inganta lafiyar dan Adam.

Kamfanin Gerawa ya fara biyan ma’aikatansa mafi ƙarancin albashin N70

Alhaji Ibrahim Muhammad Gerawa ya kuma ba da tabbacin kamfanin Gerawa zai cigaba da tallafawa duk wani al’amari da ya shafi al’umma kasancewar kamfanine yan kasa don haka ya zama wajibi kamfanin ci gaban da tallafawa daidaikun jama’a ko kungiyoyin al’umma dake jihar kano da kasa baki daya.

” Bayan daukar nauyin tafsirai da sauran karatuttukan Musulunci, Mun ga dacewar fadada irin waɗannan aiyuka don dai al’ummar da muke cikinsu su amfane mu ta fannoni daban-daban”.

Talla

Alhaji Ibrahim Gerawa ya kaddamar da wasan ne tsakanin Unity Bank da kuma FCMB, idan aka Tashi wasan 3-1.

A sanarwar da ya aikowa kadaura24, mai taimakawa kamfanin kan harkokin yada labarai Kwamaret Babangida Mamuda Biyamusu ya ce Shugaban rukunonin kamfanin na Gerawa Alhaji Dr. Ibrahim Muhammad Gerawa ya sami rakiyar mataimakinsa Alhaji Dr. Abubakar Gwadabe da Manajan Gerawa Rice Mills Alhaji Isyaku Muhammad

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...

Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano

Daga Nazifi Dukawa     Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano...

Gwamnatin Kano Ta Kammala Aikin Gina Mayanka ta Naira Biliyan 1.5

Daga Zakaria Adam Jigirya     Gwamnatin jihar Kano ta karkashin Shirin...

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...