Sarki Sanusi II ya yi raddi masu sukarsa game da sanya kafet mai sunan “Muhammadu” a dakin karantunsa

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Sarkin Kano na 16 Muhammad II, yayi taddi ga masu sukarsa game da kafet din da aka sanya a dakin karantunsa na gidan Rumfa dake dauke da sunansa, ” Mai martaba Sarkin kano Khalifa Muhammadu Sanusi II”.

A wani video mai kimanin mintinu 12 da Kadaura24 ta gani a shafukan sada zumunta, sarki Sanusi II ya ce wadanda suke sukarsa akan batun basu fahimce shi ba ne, Inda ya bayyana wasu hujjojin da Ke nuni da cewa sanya kafet din ba laifi ba ne.

” Na ji wasu malamai suna Kalubalantarmu akan wannan batun, Kuma na ji sun kawo hujjojinsu daga cikin mukhtasar, amma na fahimci ba su gina hujjojinsu akan fikihu ba”.

Yanzu-yanzu: Kotu ta yanke hukunci a karar nemen tsige Ganduje daga shugabancin APC na ƙasa

Ya ce a jikin kafet din mai martaba Sarkin kano Khalifa Muhammadu Sanusi na II aka rubuta ba wai Annabi Muhammad Salallahu Alaihi Wassalam ake nufi ba.

Sarkin ya kawo nassi da fahimtarsa game da irin saka sunan, ya kuma Kawo hujjar cewa in dai ba Muhammad Salallahu Alaihi Wassalam aka saka ba ko a jingina wani sunan dake nuni da martabar Annabi babu kuskure dan an saka suna, domin ba manufar Annabi Muhammad Sallahu alaihi wasallam ake nufi ba.

” Ina da hujjojina duk wanda yake so ya duba littafin Mukhtasar Khashiyatu dauki akan dardir ko Khashiyatu Sawi akan shehun sagir domin ganin hujjojin na wa”.

Ban take sunan Annabi Muhammadu a kafet dina ba, domin sunana ne a jiki, kuma duk me ganin yana da hujjar da tafi tawa a shirye nake dana bi maganarsa. Cewar Lamido.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Nan gaba kadan za mu bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya – Babban Hafsan tsaro

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce...

Wasu yan daba sun ajiye Makamansu a Kano

Gwamnatin Jihar Kano Hadin gwaiwa da Rundunar Yansandan Jihar...

Masu Mukamai a gwamnatin Kano ba su da uzurin kin taimakawa yan Kwankwasiyya – Sanusi Bature

Mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin...

Magoya bayan Barr Ibrahim Isa (Matawallen Gwagwarwa) sun aikawa Gwamnan Kano Budaddiyar Wasika

Daga Isa Ahmad Getso Kira don nemawa Barr. Ibrahim Isa...