Ganduje ya musanta kitsa yadda za’a sake tsige sarki Sunusi II

Date:

 

 

Shugaban jamiyyar APC a Najeriya kuma tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya musanta wani batu da ake yaɗawa cewar yana kitsa yadda za’a tsige sarkin Kano na 16 Muhammadu Sunusi II.

Wannan ya biyo bayan wasu rahotanni da suka karaɗe shafukan sada zumunta dake cewar Ganduje na yin wani sabon shiri domin sake tsige sarki Sunusi.

Obasanjo, IBB, Abdulsalami na kokarin ganin Atiku da Obi sun maye gurbin Tinubu a 2027

Idan ba’a mantaba an tsige sarkin Kano Muhammadu Sunusi II a zamanin mulkin tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje wanda a yanzu shine shugaban jamiyyar APC na Najeriya.

A wata sanarwa da ya fitar a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya yau Alhamis ta hannun Chief Oliver Okpala babban mai taimaka masa a fannin wayar da kan jama’a Ganduje ya nesanta kansa batun da ake yaɗawa cewar yana shiyra yadda za’a sake tsige sarkin Kano na 16 Muhammad Sanusi II.

Bayan sauke Kantomomin kananan hukumomin, gwamnan kano ya bayyana wadanda za su mikawa ragamar

Sanarwar ta ce Ganduje bashi da wata alaka da batun naɗawa ko tsige Muhammadu Sunusi II. Ya ce yakamata jama’a su sani cewar a yanzu ba shine gwamnan Kano ko kakakin majalisar dokoki ba, don haka babu abinda ya shafeshi da sha’anin sarautar Kano.

Sanarwar ta ci gaba da cewa abin dariya ne Ganduje wanda ya bar mulkin Kano sama da shekara guda da ta wuce amma a rika zarginshi da kitsa yadda za’a tsige ko naɗa sarki domin shi yanzu hankalinsa yana kan shugabancin da yake na jamiyyar APC da kuma bata gudunmawa.

RFI

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Bam ya fashe a Kano ya hallaka wasu ya kuma jikkata wasu

Aƙalla mutum biyar ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin...

Kotu a Kano ta sami wani Tela da laifin takurawa makwabtansa da karar keken dinki

Wata kotu a Kano ta samu wani tela da...

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...