Daga Rabi’atu Yunusa Adam
Gwamnatin jihar Kano ta ayyana ranar Litinin 23 ga watan Satumba a matsayin ranar hutun takutaha.
A wata sanarwa dauke da sa hannun Abba Danguguwa, babban sakataren ma’aikata na ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, ya ce an ba da hutun ne domin tunawa da zagayowar ranar sunan manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam.
Obasanjo, IBB, Abdulsalami na kokarin ganin Atiku da Obi sun maye gurbin Tinubu a 2027
An dai haifi manzon Allah sallallahu alaihi wasallam a ranar 12 ga Rabi’ul Auwal.
Al’ummar jihar Kano na gudanar da bukukuwan a ranar Takutaha, domin murnar haihuwar Annabi Muhammad Sallahu alaihi wasallam.
Takutaha, wani biki ne na tarihi da aka dade da yi tsawon shekaru aru-aru.
Nigerian Tracker