Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
A wani yunkuri na kau da shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027, tsoffin shugabannin Najeriya uku, Olusegun Obasanjo, Ibrahim Babangida, Abdulsalam Abubakar da manyan hafsoshin soja sun fara kokarin tasa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a gaba domin ceto kasar a zabe mai zuwa.
Har ila yau, a cikin jerin masu ruwa da tsakin da suka yi ganawar sirri a Minna a karshen makon jiya, akwai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, Mista Peter Obi.
Manyan jami’an sojojin sun nuna damuwa kan halin da jam’iyyar adawa ta PDP take ciki, Sannan sun fara neman tsohon gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike da abokansa da su zo domin ceto jam’iyyar daga rugujewa.
Warwarar zare da abawa kan dambarwar NNPCL da matatar mai ta Dangote
Jaridar Kadaura24 ta ruwaito cewa tsofaffin shugabanni uku masu fada a ji da kuma tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Janar Aliyu Gusau (Rtd) sun gana a Minna babban birnin jihar Neja a kwanan baya don tsara yadda za su karbe jam’iyyar.
Kamar yadda wata majiya mai tushe ta bayyana cikakken bayanin taron, taron manyan hafsoshin sojojin masu ritaya na da manyan ajanda biyu da suka hada da ceto tsarin jam’iyyar daga hannun Wike da kuma neman wanda ya dace da zai iya kayar da shugaba mai ci Bola Ahmed Tinubu.
Majiyar ta bayyana wa Platinumpost cewa manyan hafsoshin sojojin sun damu da yadda al’amuran jam’iyyar PDP ke tafiya a ƙasar , inda suka yanke shawarar haduwa da juna da nufin tsara hanyar da za a bi domin samun ci gaba jam’iyyar.
Bayan sauke Kantomomin kananan hukumomin, gwamnan kano ya bayyana wadanda za su mikawa ragamar
Tsoffin shugabannin mulkin sojan da aka ce ba su gamsu da salon mulkin shugaba Tinubu ba, tuni suka fara laluben dan takarar shugaban kasa mai inganci gabanin zaben 2027.
Idan dai za a iya tunawa IBB da Obasanjo da Gusau su uku ne suka jagoranci kafa jam’iyyar PDP a shekarar 1998.
Don haka, sun tuntubi tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark da nufin karbar shugabancin jam’iyyar PDP daga Umaru Iliya Damagun wanda abokin Ministan babban birnin tarayya ne.
PlatinumPost ta tattaro cewa lokacin da aka fara tuntubar David Mark wanda ke hutu a Amurka ya ki amincewa da aikin ceto PDP daga halaka.
Tsohon shugaban majalisar dattawa kuma gwamnan mulkin soja na jihar Neja, haifaffen Benue, a karshe ya amince da bukatar Janar Babangida da ake ganin shi ne ubangidansa kuma wanda ya taimaka masa.
Majiyar ta jaddada cewa “Janar-Janar din a taron da suka yi a Minna suna son Devid Mark ya kasance wanda zai ja ragamar jam’iyyar PDP yayin da suka fara laluben sahihin dan takarar shugaban kasa wanda zai kayar da Tinubu a 2027,”
An tattaro cewa a zauren taron sirrin, mutane uku IBB, Abdulsalam da Gusau sun aminta jam’iyyar PDP ta baiwa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar takarar shugaban kasa, yayin da Obasanjo ya zayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP). ), akan zaben 2023 Mr Peter Obi.