Sojojin Nigeria sun Kashe Ƙasurgumin Dan ta’adda da ya addabi Arewacin Nigeria

Date:

 

Rahotanni daga majiyoyinta a jihar Zamfara sun tabbatar da kisan Halilu Buzu wanda aka fi sani da Halilu Sububu wanda shi ne ƙasurgumin ɗanbindigar da jami’an tsaron Najeriyar ke nema ruwa a jallo.

Sojojin dai sun samu nasarar kisan ɗanbindigar ne bayan ɗauki ba ɗaɗi tsakaninsu da wani gungun ƴan bindiga a tsakanin kwanar Dogon Ƙarfe zuwa Mayanci a ƙananan hukumomin Zurmi da Anka.

Ɗanjarida a yankin wanda ya tattaro bayanai kan abin da ya faru, Mannir Fura Girke ya shaida wa BBC yadda al’amarin ya faru.

“Jami’an tsaro sun samu bayanan sirri da ke nuna cewa ƙasurgumin ɗan bindiga Kachalla Halilu Sububu zai wuce da tawagarsa. Yana tafiya da rakiyar ƴanbindiga fiye da 60 kuma inda tun Magribar yammacin Alhmais har zuwa asubar yau Juma’a.

A nan ne kuma aka wannan ba-ta kashi kuma sojoji suka samu damar kashe shi tare da manyan kwamandojinsa bayan samun nasarar karɓe babura fiye da 20 da alburusai da sauran nau’in makamai.” In ji Fura Girke.

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da hakan a shafinta na X, inda babban hafsan sojojin Najeriyar, Janaral Christopher Musa yake shaida wa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Dare cewa “kwanan Bello Turji da sauran ƴan ta’adda ya ƙare kuma ya kamata kisan Halilu Sububu ya zama izna gare su.”

Wani bincike da jaridar PRNigeria ta yi ya nuna cewa Halilu Sububu ne ya kitsa kisan matuƙin jirgin nan mara matuƙi na hukumar farin kaya ta DSS kimanin watanni biyu da suka gabata.

Yanzu-yanzu: An rage kudin shiga zaɓen kananan hukumomi na Kano

Wane ne Halilu Sububu?

Ɗanjarida Mannir Fura Girke wanda ke bibiyar al’amuran ƴan bindiga a yankin jihohin Zamfara da Sokoto ya faɗi abubuwa guda shida a kan shi wannan ɗan bindiga:

Halilu Buzu ko kuma Halilu Sububu ko kuma Kachalla Halilu Tubali.

Shi ne madugu ko shugaban ƴanfashin daji da ke arewa maso yamma baki ɗaya da ke kisa da satar jama’a.

Halilu ya shahara wurin fataucin makamai.

Gawar dan ta’adda Halilu wanda sojoji suka kashe

Ya yi ƙaurin suna wajen haƙar ma’adanai kamar gwal da safararsu zuwa ƙasashen waje.

A kwanakin baya sojojin Najeriya suka ayyana shi a ɗan ta’addan da suke nema ruwa a jallo.

Jami’an tsaro sun ce Halilu Sububu ko Buzu ɗan jamhuriyar Nijar ne.

Asibitin Best Choice Ya Kaddamar Da Sabuwar Na’urar Jarirai Ta (Jaundice) Irinta Ta Farko A Arewacin Najeriya

Me kisan Kachalla ke nufi?

Ɗanjarida Mannir Fura Girke ya shaida wa BBC cewa “wannan babbar nasara ce ba wai ga jami’an tsaro ba har ga kowa da kowa. Misali yanzu girbi za a fara amma ɓarayin mafi yawanci yaran Halilu sun hana jama’a. Ka ga kenan yanzu dole ko dai su bar jama’a su je gona ko kuma su bar yankin baki ɗaya.”

Muna ganin kisan Halilu tamkar an yi jana’izar ta’addanci ne a arewa maso yammacin Najeriya domin shi ne madugunsu gabaɗaya.” In ji Danjarida Fura Girke.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...