Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Sarki Charles III na burtaniya ya tarbi bakuncin Shugaban ƙasar Nigeriya Bola Tinubu a ranar Laraba a fadar Buckingham da ke birnin Landan na Inda suka yi ganawar sirri.
Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce taron ya nuna kyakkyawar alakar da ke tsakanin Najeriya da Burtaniya.
Ya ce wannan shi ne ganawar farko da shugabannin biyu suka yi tun bayan da suka hadu a Dubai a taron COP 28 na yanayi a bara.
Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kano ta Sanya Ranar Komawa Makarantun Firamare da Sakandire
Sanarwar ta ce Sarkin ne ya bukaci ganawa da shugaban Tinubu.
“Shugabannin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi al’amuran duniya da na shiyyar Africa, inda suka mai da hankali kan kalubalen sauyin yanayi,” in ji Onanuga.
Ya ce Tinubu da Sarki Charles sun kuma binciko damar yin hadin gwiwa tare da sa ran taron COP 29 da za a yi a Azerbaijan da kuma taron shugabannin kasashen Commonwealth (CHOGM) a Samoa.
Amb. Jamilu Bala Gama ya Zama Sabon shugaban kasuwar waya ta Farm Center
Shugaba Tinubu ya sake nanata kudurin Najeriya na ganin an magance matsalar sauyin yanayi ta hanyar da ta dace da manufofin tsaron makamashin kasar yayin da yake tabbatar da shirin Najeriya na daukar dabarun da sauran kasashen duniya ke amfani da shi
Onanuga ya ce “A yayin tattaunawar tasu, shugabannin biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan sabbin hanyoyin samar da kudade tare da bayyana sha’awar juna na karfafa hadin gwiwa ta hanyar amfani da matsayin shugabancin Najeriya a Afirka da kuma Commonwealth,” in ji Onanuga.
Solacebase