Zaɓen Kano: NDLEA ta fitar da sakamakon yan takara 20 da aka yiwa gwajin shan kwaya

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce sun yiwa mutane 20 da ke neman kujerar shugabannin kananan hukumomi a jihar Kano gwajin kwaya da sauran kayan maye gabanin zaben kananan hukumomi da ke tafe.

Kwamandan NDLEA a jihar, Abubakar Idris Ahmad, ya ce masu neman takarar da jam’iyyar NNPP mai mulki ta gabatar a jihar an yi musu gwajin kwayoyi har ma da hotar iblis da dai sauransu.

Jerin sunayen yan takara 38 da NNPP ta tsayar a zaɓen shugabannin kananan hukumomin Kano

Ahmad ya bayyana cewa, duk da cewa babu mace ko daya da suka yiwa gwajin ya zuwa yanzu, amma ana ci gaba da gudanar da aikin tantancewar, kuma ana sa ran za a yi wa sauran ‘yan takarar gwajin kafin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC) ta yi musu nata.

Shugaban hukumar ta NDLEA a Kano ya ce duk cikin wadanda suka tantance din ba a sami ko mutum daya mai shan kwaya ko wani Abu mai bugarwa ba.

Idan dai za a iya tunawa, hukumar ta KANSIEC ta tsayar da ranar 26 ga Oktoba, 2024, inda za a fafata a kujerun shugabanni 44 da na kansiloli 484.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...