Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mazauna garin Maiduguri da ruwa daga madatsar ruwa ta Alau ya raba da muhallansu sun fara komawa gidajensu yayin da ruwa ke raguwa a hankali.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa da yawa daga cikin wadanda ambaliyar ta shafa da suka kwana a waje sun ce duk da ruwan ya lafa, ba su iya tantance asarar da suka yi ba.
“Muna gaggawar mu koma gidajenmu don ganin abin da ya rage a gidajenmu, don dauke wasu daga cikin dukiyoyinmu da suka rage,” in ji Ali Bana na gundumar Gwange.
Musa Abdullahi na unguwar Gomari, ya ce ya samu damar zuwa gidansa.
“Daga abun da na gani har yanzu gidana yana cike da ruwa. Don haka dole mu sake yin kwanaki a waje kafin mu koma ciki,” in ji Abdullahi.
A halin da ake ciki kuma, wani rahoton halin da ake ciki kan ambaliyar da ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya OCHA ya fitar, ya ce fiye da mutane 239,000 ne ambaliyar ta shafa.
Jerin sunayen yan takara 38 da NNPP ta tsayar a zaɓen shugabannin kananan hukumomin Kano
Ambaliyar ta tilastawa wasu daga cikin mutanen da abin ya shafa kaura zuwa sansanin ‘yan gudun hijira na Muna, wanda yake dauke da ‘yan gudun hijira sama da 50,000.
“Jami’an gwamnati sun rika kwashe al’umma daga Inda ruwan yafi hatsari zuwa wasu warare da ruwan bai kai ba,” in ji rahoton.
NAN ta ruwaito cewa ambaliyar ruwan ta shafi hanyoyin sadarwa, wutar lantarki da ruwan sha a mafi yawan sassan garin. (NAN)