Zaɓen 2027: Kwankwaso Ya Bugi Kirji

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Dr Rabiu Kwankwaso, ya ce zai shi ne lashe zaben shugaban kasa a 2027.

Kwankwaso, Wanda ya yiwa jam’iyyar takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya yi wannan furuci ne a ranar Asabar a lokacin da ya kaddamar da sakatariyar jam’iyyar NNPP, a kan titin IBB, Katsina.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa ya je Katsina ne domin ziyarar ta’aziyya ga iyalan ‘Yar’aduwa bisa rasuwar mai mahaifiyarsu, Hajiya Dada.

Dalilin da yasa mai magana da yawun Shugaban ƙasa Tinubu ya Ajiye aikinsa

A cewarsa, jam’iyyar a shirye take ta karbi ragamar shugabancin kasa, jihohi da sauran mukamai a fadin kasar nan zuwa 2027.

Ya bayyana cewa jam’iyyar na kan hanyar samun nasara a babban zaben 2027.

Jagoran na Kwankwasiyya ya ce, “Ina so in tunatar da ku cewa, jam’iyyar PDP ta riga ta mutu, da muna cikin jam’iyyar, amma tunda muka ga sun fita daga kan layi, sai muka yanke shawarar ficewa daga cikinta.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya musamman mata da matasa da kada su bari a yaudare su da taliya ko kudi a lokacin zabe mai zuwa.

Yadda jami’ar Maryam Abacha ta Samar da shugabannin makarantun aikin jinya 5, lauyoyi 100 da wasu a Shekara 12

Kwankwaso ya kuma yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su kara himma wajen samun nasarar jam’iyyar a jihar da kasa baki daya.

Ya yaba musu da sauran masu ruwa da tsaki a jihar kan gyaran sakatariyar jihar, inda ya ce hakan na daga cikin shirye-shiryen samun nasara.

Kwankwaso ya kuma yi alkawarin tallafa wa wani karamin yaro Abubakar Ibrahim na yankin Yammawa a jihar, wanda ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...

Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano

Daga Nazifi Dukawa     Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano...

Gwamnatin Kano Ta Kammala Aikin Gina Mayanka ta Naira Biliyan 1.5

Daga Zakaria Adam Jigirya     Gwamnatin jihar Kano ta karkashin Shirin...

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...