Daga Aminu Bala Modobi
Rahotanni na nuni da cewa al’ummar garin Imawa dake karamar hukumar Kura a jihar Kano sun rufe titin Kano zuwa Zaria.
Kadaura24 rawaito cewa wasu mazauna garin sun bayyana cewa sun dauki matakin rufe hanyar ne sakamakon yadda wata mota ta buge wasu mutane da suka taso daga Sallar Juma’a.
Motar yayin da take tsaka da tafiya ta kwacewa direban, inda ta kutsa kai tareda danne Massallatan yayinda aka gaggauta kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin kulada lafiyar su.
An rawaito cewa nan take mutane 7 suka rasa rayukansu, yayin da wasu kuma suka jikkata.
Mafi Ƙarancin Albashi: Majalisar dokokin Kano ta amince da kwarya-kwaryar kasafin kuɗi na N99b
Tuni dai wasu daga cikin mutanen garin suka sanya wa motar da ta buge masallatan wuta inda suka ƙone ta ƙurmus.
“Sun sanya wa motar wuta ne a kan titi sannan suka kashe kan hanyar sakamakon zargin bige musu ƴan uwa da wata mota ta yi. Inda mutane 7 suka mutu sakamakon hatsari”, in ji wata majiya dake wurin
Wani matafiyi dake hanyar ya shaida mana cewa fiye da awa uku ke nan hanyar Kano zuwa Zaria take a rufe sakamakon wancan hadari.
Kotu ta tusa keyar alƙalin bogi zuwa gidan yari a Kano
Majiyar ta ƙara da cewa; “masu motoci dai sun yi jungum-jungum, inda lamarin ya shafi dubban matafiya. Komai ya tsaya cik ba abin da ke motsi.”
Idan za’a iya tunawa makwanni shida da suka gabata, wata mota ta buge mutane da dama a lokacin da suke sallah Juma’a a dai garin na Imawa dake karamar hukumar