Daga Isa Ahmad Getso
Uwar jam’iyyar PDP ta kasa ta tsayar da ranakun da za a gudanar da zabukan shugabanninta tun daga mazabu kananan hukumomi da kuma juhohi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren tsare-tsare na jam’iyyar na kasa Umar M Bature ya sanyawa hannu.
Sanarwar ta ce jam’iyyar PDP ta sanya Ranar Asabar 7 September 2024 za’a gudanar da zaben Shuwagabannin jam’iyya na Mazabu .
Mahaifiyar tsohon shugaban Nigeria ta rasu
Ranar Asabar 21 September 2024 za’a gudanar da zaben shuwagabannin kananan hukumomi .
Ranar 05 October 2024 za’a gudanar da Zaben shuwagabannin jam’iyya na Jihohin Nigeria .
![Talla](https://kadaura24.com/wp-content/uploads/2024/08/IMG-20240821-WA0004-211x300.jpg)
Sanarwar ta bukaci yan Jam’iyyar da su tabbatar sun gudanar da zaben shuwagabannin cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.