Allah ya yiwa Hajiya Dada Yar’Adua rasuwa a yau Litinin.
Hajiya Dada Yar’adua Uwar Shugaban Kasa Da Mataimakin Shugaban Kasa, Kuma Kakar Minista Da Matan Gwamnoni Uku
Mijinta Musa ‘Yar’Adua tsohon minista ne, sannan kuma ita ce ta haifi tsohon mataimakin shugaban kasa a 1976- 1979, wato Marigayi Shehu Musa ‘Yar’adua,
Farashin kayan abinci na daf da karyewa a kasuwa — Kwastam
Haka kuma ita ce mahaifiyar tsohon gwamnan da ya yi shekara takwas a jihar Katsina (Marigayi Umaru Musa ‘Yar’Adua) 1999 -2007 daga bisani ya zama shugaban kasa daga shekarar 2007-2009.
Jikanta ya yi minista a 2009-2011 sannan kuma jikokinta mata guda uku suna auren tsoffin gwamnoni kasar nan, wato na Kebbi, Bauchi da Katsina.