Daga Rahama Umar Kwaru
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa ƙasurgumin dan daban da ya addabi unguwar Dorayi dake karamar hukumar Gwale a jihar Kano Abba Burakita ya mutu.
Ya mutu ne sakamakon faɗa da wasu ƴan daba a unguwar Ɗorayi.
Kakakin Rundunar ‘Yan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce Barakita yana daga cikin ‘Yan daban da suke nema ruwa a Jallo.
2027: Atiku Obi da Kwankwaso sun fara tattaunawa – PDP
Wanda a karshe, ya mutu bayan da aka kai shi Asibitin Murtala likitoci suka tabbatar da cewa ya Mutu.
Burakita yana cikin yan sandan sarauniya da ya rungumi zaman lafiya a 2023 amma ya koma ruwa.