Cigaban karamar hukumar Rano ne ya sa na fito takarar ba don kashin kaina ba – Dr. Isma’il Yusuf Musa

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Guda cikin yan takarar kujerar shugaban karamar hukumar Rano a tutar jam’iyyar NNPP Dr. Ismail Yusuf musa ya bayyana cewa ya fito takarar ne domin ya bada ta shi gudunnawar wajen ciyar da karamar hukumar gaba.

” Akwai manufofi da nake da su wadanda nake ganin idan Allah ya bani dama kuma na aiwatar da su babu Shakka karamar hukumar Rano sai ta zama abar kwatance ta fuskar, aiyukan Raya kasa da bunkasa rayuwar jama’a”.

Dr. Isma’il Yusuf ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da wakilin kadaura24 ranar juma’ar.

Talla
Talla

Yace tabbas Kwankwasiyya tana da kyawawan manufofin cigaba, to amma zai kara na shi manufofin domin dai a samu lungu da sako na karamar hukumar Rano su san cewa ana yin dimokaradiyya.

” Daga cikin manufofin nawa akwai na aiyukan Raya kasa, garin mu na Rano babban gari ne ya kamata a yanzu ace Muna da aiyukan raya kasa biye da yadda muke da su a yanzu, don haka zan tabbatar kowacce mazaba ta sami aiyukan tituna da futilun solar da magudanan ruwa masu inganci da dai sauransu”. Inji Dr. Isma’il Yusuf

Sabuwar badakala: Ana zargin gwamnatin Kano da sake sayar da filin Idi

“Zan fito tsari na musamman da zai ba da damar inganta asibitocinmu da samar da magunguna kyauta ga al’umma don inganta lafiyar al’ummar mu”.

Ya ce dama harkar ilimi ita ce gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf tafi baiwa fifiko, don haka ya ce shi ma zai dora akan kokarin gwamnan don ganin an sake inganta fannin yadda ya kamata.

Dr. Isma’il Yusuf Musa ya kuma ce zai duk mai yiwuwa don ganin ya inganta rayuwar mata da matasan Rano saboda muhimmancin da suke da shi, ta hanyar koya musu sana’o’i da basu jari duk wata.

“Akwai tanade-tanade masu tarin yawa da na yiwa al’ummar karamar hukumar Rano, kawai Ina fatan su ta yi addu’o’i har Allah ya tabbatar mana da damar domin mu hidimta musu kamar yadda jagoranmu Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya hidimtawa al’umma jihar kano”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...