Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Rahotanni na nuni da cewa gwamnatin jihar kano karkashin hukumar tsarawa da raya burane ta jihar KNUPDA tana sake yanka filin Idi tare da sayar da shiga ga al’umma.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 tun a watan yuni na Shekarar 2023, gwamnatin jihar Kano ta rushe shagunan da aka gina a ciki da wajen masallacin idi na Kofar Mata, bisa zargin gwamnatin Ganduje da rashin kishi wajen sayar da filin mai tarihi.
Dama dai gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta yi alkawarin rushe shagunan tun lokacin da take yakin neman zaben shekara ta 2023.
Amma daga shekaran jiya zuwa yau zargi yayi karfi cewa gwamnatin ta fara yanka shagunan tare da sayar da su ga wasu yan kasuwa , kamar dai yadda gwamnatin da ta gabata ta Ganduje ta yi.
Na fi damuwa da kuncin rayuwar da yan Nigeria suke ciki fiye da takara a 2027 – Atiku Abubakar
Da safiyar wannan rana ta alhamis Dr. Bello Habib Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello ya tabbatar da wancan zargi ta hanyar fitar da wasu takardu masu dauke da shedar hukumar KNUPDA, Inda aka sayar da filayen ga wasu mata.
” Malam Rukayya ta sayi filin kwantena mai lamba 135 akan kudi Naira 330, haka ita ma malama Khadija ta sayi wani filin kwantena mai lamba 111;akan kudi Naira 330″. A cewar Rahoton Dan Bello.

Dan Bello dai ya sanya dukkanin takardar sayar da filayen tare da shaidar biyan kudi wanda Khadija da Rukayya suka biya a ranar 10 ga watan Yuli, 2024.
Da yake mayar da martani shugaban hukumar tsara Birare na Kano Arch. Ibrahim Yakubu ya ce zargi sayar da filin Idin na kofar mata ba gaskiya ba ne bashi da tushe ballantana makama.
” Babu wata magana ta sayar da filin Idin na kofar mata, hasali ma Cibiyar addinin Musulmi za mu yi wadda zata dauki Abubuwa da dama na harkokin Addinin Musulunci”.
Ya ce zargi kagene da kokarin bata sunan gwamnatin jihar kano a Ido duniya.

Ko a kwanakin baya sai da Dan Bello ya bankado wata badakalar magunguna da Ake yi a wasu daga cikin kananan hukumomin jihar kano.
Lamarin da ya sa gwamnan kano ya ce bashi da masaniya kan batun kuma ya ba da umarnin a bincika, wanda hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar ta gano wasu kudaden tare da kama wasu cikin wadanda ake zargi.