Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bar jihar kano zuwa Abuja, a karon farko tun bayan dawowarsa jihar a watan Mayu.
Wata majiya ta bayyana cewa, sarkin ya tafi wata ziyarar aiki a Abuja domin halartar wani babban taro da ya kunshi sarakuna.
Gwamnatin Kano za ta rika samar da Naira biliyan daya a duk shekara daga bangaren ma’adinai
Kadaura24 ta ruwaito cewa Aminu Ado Bayero ya koma Kano kwanaki kadan bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke shi daga kan karagar, kuma tun a wancan lokaci yake Kalubalantar cire shin a gaban Kotu.
Tun ranar 20 ga watan Yuli da sarkin ya halarci taron yiwa kasa addu’o’in samun zaman lafiya a gidan Marigayi Sheikh Ishaq Rabi’u dake goron Dutse, sarkin bai sake fita ba sai wannan rana ta juma’a da ya fita zuwa ban-ban birnin tarayya Abuja.
Sabuwar Badakala a Kano: An kama Kantomomi 3 da wasu 19, An kuma Saki Dan Kwankwaso
A halin yanzu dai ba sarki a Kano domin shi ma Sarki na 16, Muhammadu Sanusi na II ya yi tattaki zuwa kasar Ingila inda ya je domin kare karatun digirinsa na digirgir.
An hango Aminu Ado Bayero a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja tare da Oni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, da dai sauransu.
Ga wasu daga hotunan yadda fitar ta kasance: