Shugaban Hukumar hana almubazzaranci da dukiyoyin al’ummar da sauran Laifuka ta kasa (ICPC) Dr Musa Adamu Aliyu ya shawarci ‘yan jarida da ke Kano da su rika mai da hankali wajen yin rahotanni da za su bunkasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.
Musa Aliyu ya bayyana haka ne a yayin wani horo na yini guda da aka shiryawa yan jaridun da ke yada labarai ta yanar gizo a karkashin kungiyarsa ta ASKOJ a Kano.
Ya ce idan aka yi la’akari da abubuwan da suka faru a kasar nan akwai bukatar ‘yan jarida su rika ba da labarin abubuwan ci gaba da za su daukaka martabar kasar a duniya, maimakon bayar da rahoton ayyukan tada kayar baya da sauran abubuwan da ba su dace ba.
Badakalar magunguna: Abubunwan da muka gano bayan kama Dan Kwankwaso da wasu mutum 4 – Muhuyi Magaji
Shugaban hukumar wanda ya samu wakilcin mataimakin kwamishinan ICPC Hassan Salihu, ya ce hukumar ta ga ya zama dole ta hada kai da dan jaridun yanar gizo domin su san abubuwan da ake bukata na bayar da rahoton ayyukan ICPC .
Ya kuma bukaci yan jaridan da su rika kiyaye ka’idoji da dokokin aikin jarida a koda yaushe, kuma su kaucewa yada labarai karya tare da yin Adalci a cikin rahotonninsu domin cigaban kasa.
Shugaban ICPC ya bayyana cewa, kyakkyawar alakar da ke tsakanin dan jaridar ta yanar gizo da hukumar abin a yaba ne, don haka ya kamata a kara himma wajen dorewarta domin ciyar da Nigeria gaba.
A nasa jawabin shugaban kungiyar ‘yan jaridu yanar gizo Yakubu Salisu ya yabawa hukumar ta ICPC bisa shirya wannan bita ta kwana daya ga yan jaridun dake aiki a yanar gizo.
Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya cika shekaru 63 a duniya
Ya bayyana cewa an kafa kungiyar ne a shekarar 2020 da nufin hada kan ‘yan jaridan domin cimma manufofin da aka sa gaba.
Yakubu Salisu ya bukaci mahalarta taron da su yi amfani da damar da suka samu domin bunkasa aikinsu a yada labarai.
A yayin horon an gabatar da kasidu daban-daban da suka shafi aikin hukumar.
Taron ya samu halartar masu jaridun yanar gizo daban-daban a Kano