Daga: Safwan Suraj Ilyas
Al’ummar Unguwar Ja’en da ke jihar Kano sun gudanar da salloli na musamman da addu’o’in Alkunut domin neman sauki daga Allah game da halin kuncin rayuwa, yunwa da tsadar Kayan Masarufi da ake fama su a Najeriya.
Jama’ar unguwar, wadanda su ka hadarda Maza da Mata da akasarin su matasa ne sun gudanar da Sallar da addu’o’in ne a filin Yusra da ke Unguwar ta Ja’en Makera da Safiyar Ranar lahadim da ta gabata wanda, Limamin babban Masallacin unguwar Mal. Umar Sulaiman Lalu ya jagoranta domin samun samun agaji daga Allah kan halin da Yunwa da fatarar da ake ciki.
Hakan na zuwa ne biyo bayan hukuncin bayan taro da kwamitin zaman lafiya na Unguwar Karkashin jagorancin Alh. Almu Wada Jaen Makera su ka gudanar a lokacin da unguwar tai fama da rikice-rikicen daba da ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi a kwanakin baya.
Gwamnan Abba Gida-gida ya yi alkawarin samar da Karin birane biyu a Kano
Shugaban ya roki al’umma da su zauna lafiya da juna inda yai kira ga mawadata da su tallafi masu karamin karfi don ta haka ne kadai za’a magance dukkan matsalolin dake addabar yankin.
“Zaman lafiya zai samu ne kadai yayin da mawadata suka tallafi marasa karfi ta hanyar basu ilmi, abinci da koya musu sanao’in hannu don dogaro dakai” in jishi
Daya daga cikin matasan da suka shirya taron addu’o’in, Idris Bala (Abba) ya ce, “An shirya wannan taro a lokacin daya dace kasancewar matasa na cikin firgici da damuwar rashin sanin makomarsu sakamakon tsadar rayuwar da ake ciki inda yai kira ga shugabanni da su ji tsoron Allah su kyautatawa rayuwar matasa” in jishi
Daya daga mazauna yankin na ja’en Makera Sharani Maifada wanda ya halarci taron ya bayyana kaduwarsa bisa irin yadda rayuwa ke kara tsada ta yadda yake da burin komawa makaranta a wannan shekarar amma sakamakon yadda rayyuwa tai tsada yasa sana’ar sa da yake ta kafintanci ba zata iya rikeshi kuma ta bashi kudin makaranta ba kasancewar aikin baya samuwa kamar a baya.
Dawo da tallafin mai: Atiku ya yiwa Tinubu martani mai zafi
Itama wata matashiya data bukaci a sakaya sunanta tai kira ga shugabanni dasu tausayawa mata ta hanyar tallafa musu da abinci don gudun afkawar su cikin ayyukan masha’a “A baya muna iya cin abinci akalla so uku a rana amma a sakamakon matsin tattalin arziki a wallahi yanzu dakyar muke samu muci sau daya gashi ko makaranta mun hakura da ita” in jita.
Manya masu fada aji da dama daga sassan unguwar ta jaen makera ne suka halarci taron inda akai kiran “yan kasuwa dasu sassauta farashi don samun dacewa duniya da lahira.