Hukumar karbar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta fara bincike kan badakalar sayen magunguna na biliyoyin nairori a kananan hukumomi 44 na jihar.
Shugaban hukumar Muhuyi Rimin-Gado ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ta wayar tarho a Kano ranar Talata.
“Mun fara bincike mai zurfi kan zarge-zargen da ake yi game da samar da magunguna na biliyoyin Naira ga kananan hukumomi 44.
Fadan daba/Tsadar rayuwa: A’lummar Ja’en Makera a Kano sun gabatar da alkunut don neman daukin Allah
Rimin-Gado ya ce “Ko da wanene ke da hannu, za mu gano shi kuma mu hukunta wadanda aka samu da laifi.”
A cewarsa, hukumar na binciken zargin karkatar da kayan abinci da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati Abba Yusuf, Shehu Sagagi ya yi.
Shugaban ya yi kira ga jama’a da su bayar da sahihin bayanai da za su taimaka wajen gudanar da binciken.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Dr. Bello Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello ya bankado wata almundahana kudaden kananan hukumomin Kano 44 da ake fitar wa da sunan siyan magunguna, wanda ake zargin wani makusanci jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da mallakar kamfanin da ake amfani da shi.
Gwamnan Abba Gida-gida ya yi alkawarin samar da Karin birane biyu a Kano
Kadaura24 ta kuma rawaito cewa gwamna Yusuf a cikin wata sanarwa, ya musanta masaniya akan kwangilar da aka ce na samar da magunguna.
Kwamishinan yada labarai, Baba Halilu Dantiye, da Darakta Janar na yada labaran gwamna Sanusi Dawakin-Tofa ne suka sanya hannu akan sanarwar.
Don haka gwamnan ya umurci hukumar da ta gaggauta fara bincike kan lamarin tare da kai rahoton sakamakon domin daukar matakin da ya dace.