Rushewar gini ya kashe wasu yara biyu ƴan gida ɗaya a Kano

Date:

 

Wasu yara ‘yan gida daya sun rasa rayukansu sakamakon ginin da ya rufta akansu a lokacin da suke cikin ɗaki.

Ginin ya rufto ne sakamakon mamakon ruwan sama lokacin da yaran suke bacci.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kano ta tabbatar da mutuwar mutum goma sha takwas sakamakon ambaliyar ruwa a sassan jihar.

Mahaifin yaran ya ce bai jima da kwanciya ba sai ya ji ƙara bayan anyi wani ruwa mai ƙarfi.

Da dumi-dumi: Tinubu ya bayar da umarnin biyan tallafin man fetur – Rahoto

“Ƙarar da na ji ta girgiza ko ina sai na firgita na tashi, ina miƙe wa sai na ji ƙarar ƙaramar yarinyata tana hun wayyo Allah a danne ni,ina fitowa kawai sai naga bangon daƙin gaba ɗaya ya fadi a kansu.” in ji mahaifin.

“Duka yarana biyar ne a cikin daƙin daya rushe.”

Mahaifin ya ce moƙocin shi ne ya taimaka masa suka ɗaga wani katako inda suka samu suka fito da yara uku yayin da kuma aka kasa ceton sauran biyun.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Kano,Isiyaku Abudllahi Kubarachi ya ce ambaliyar ruwa a Kano ta yi sanadin mutuwar mutane da dama da kuma rushewar gine-gine.

NNPC Ya Magantu Kan Wahalar Mai A Nigeria

“Waɗanda suka rasa rayukansu a wannan shekarar a ƙananan hukumominmu muna da kamar mutum 18 a yanzu inda waɗansu ɗakuna ne suka faɗa musu a ka, wasu kuma gonankinsu za su je kuma guraren da akwai ruwa kuma za su tsallaka, daga nan ne ake samun matsala.” in ji shugaban.

Shugaban ya kuma ce a cikin ƙiyasinsu gabakiɗaya dai akwai mutum 8,773 waɗanda irin wannan lamarin ya shafa a jihar Kano.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...