Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma wanda ya yiwa babbar jam’iyyar adawa ta Nigeriya PDP takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce sabbin bayanai da ke zagayawa a kafafen yaɗa labarai dangane da yunƙurin Gwamnatin tarayya na cigaba da biyan tallafin mai cikin sirri, wani sabon shafi ne da ke sake fito da nuƙu-nuƙu da rashin aminci dake gudana ƙarƙashin mulkin Bola Ahmed Tinubu.
“Wannan mataki na cin karo da matsayar da shugaban ƙasa ya dauka a jawabin da ya yiwa ‘yan ƙasa, bayan zanga-zangar tsadar rayuwa da ta gabata, inda ya kafe akan cewa ba zai dawo da biyan tallafin ba”.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Atiku Abubakar ya fitar da yammacin ranar litinin din nan, a matsayin martani ga shugaba Tinubu.
“Tun kafin wannan jawabi nasa, akwai bayanai da ke cewa tuni aka cigaba da biyan wannan tallafi ta hanyar da bata dace ba. Kuma abun takai ci al’umar ƙasa na shan fetur da tsada”. Inji Atiku Abubakar
Ya ce bambanci da ake samu tsakanin abinda shugaban ke fada da kuma abubuwan da yake aikatawa na nuna irin gurɓataccen shugabancin dake gudana a ƙar ƙashin sa.
Da dumi-dumi: Tinubu ya bayar da umarnin biyan tallafin man fetur – Rahoto
“A lokacin da ‘yan ƙasa ke fama da tsadar rayuwa da kuma ƙarancin man fetur, jan ƙafar da gwamnatin ke cigaba da yi wajen buɗe matatar mai ta Patakwal abun kunya ne ga ƙasar nan, wanda kuma ya rataya akan Tinubu kai tsaye a matsayin sa na minitan harkokin mai na Najeriya.” Inji shi
Atiku Abubakar ya kara da cewa har ila yau, musun da kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) ke yi na ƙara ta’azzara wahalhalun da ‘yan kasa ke sha ta fuskar ƙarancin man fetur da tsadar sa.
“Yayin da ake gwabza muhawara tsakanin yan kasuwa na cikin gida dake goyon bayan matatun mai na ƙasa, da kuma wanɗanda ke goyon bayan cigaba da shigo da man daga kasashen waje, shirun da shugaban kasar ya yi akan wannan batun shi ma wani abun damuwa ne sosai”.
Ya ce Yana da kyau ace shugaba Tinubu, wanda ke da alhakin warware ire-iren waɗan nan matsaloli domin kare martabar ƙasa, ya fito ya samar da mafita kamar yadda ake tsammani.
Bayan Cire Shugaban NAHCON, Tinubu ya nada wani malamin Addini daga Kano
“Ɓoye ɓoyen da kamfanin mai na ƙasa ke yi akan taƙamaiman halin da ake ciki tare da rahotannin karkatar da maƙuden kudaden da aka ware su domin gudanar da wasu muhimman ayyuka zuwa biyan tallafin mai na cigaba da dagula al’amura”.
“Idan waɗannan rahotanni suka kasance gaskiya, ba shakka federaliyyar kasar nan na cikin mawuyacin hali. Saboda haka, yana da matukar muhimmanci Tinubu ya warware wannan sarƙaƙiya da gwamnatin sa ta jefa ƙasar nan a ciki a ɓangaren abunda ya shafi man fetur”. Inji Atiku
Atiku Abubakar ya ce ta hanyar gaskiya ne kaɗai za a samu mafita dangane da wahalhalun man fetur da ake fama da shi a kasar nan.