… Har yanzu akwai zarge-zarge
17 na tada hargitsi, banka wuta da kisa rataye a wuyan Doguwa
… Jibrin fayyace rikicin da ya faru a 2019
… Doguwa mutum ne algungumin da ya kamata a rufe wa baki, kowa ya huta
… Dangantaka ta da Tinubu ba ɓoyayya ba ce
…Zan cigaba da kare Kwankwaso, Abba da daga ‘yan gadangarƙama, irin su Doguwa
Na sake fitowa domin ƙara sauke nauyin maida wa Honorabul Alhassan Ado Doguwa raddin bulkarar da ya yi min a ranar 8 Ga Agusta, 2024, inda ya riƙa yin soki-burutsu da kame-kame dangane da zargin kisa da har yanzu ke rataye a wuyan sa.
A dukkan alamu Doguwa ya ɗibge, ganin yadda yake gaggawa da azarɓaɓin murnar hukunci guda ɗaya tilo da kotu ta yi, alhali kuwa a fili sanin kowa ne akwai sauran zarge-zarge har 17 da aka zarge wuyan sa da su, waɗanda suka ƙunshi tayar da hargitsi, banka wuta da kisa. Ba na shakku, ba na tababa duk tsalle-tsallen da Doguwa zai cigaba da yi, sai hukuncin kotu ya damƙo shi, an yi masa kamun-kazar-kuku.
A Karon Farko Malam Shekarau ya Magantu kan Rikicin Masarautar Kano
Ga babban misali nan kan laifin kisa da Ba’Amurke OJ Simpson ya aikata, ya isa zama darasi da ishara ga Doguwa.
Doguwa ya cika jaye-jayen waɗanda babu ruwan su a cikin kwatagwangwamar kwafsawar da nake yi da shi, musamman ma shugabannin jam’iyyar sa, a duk lokacin da na ɓallo masa ruwan da ke neman haɗiye shi dangane da yawan suka da caccaka marar dalili ko hujja da yake wa Kwankwaso.
Gaskiyar magana ita ce, wannan tarangahuma ce ta Alasan Ado Doguwa shi kaɗai. Magana ce ake yi kan irin kasassaɓar da yake yawan fesowa daga bakin sa wanda ba ya iya yi wa linzami. Saboda shi dama bai yi ilimin sanin karin maganar nan da Hausawa ke cewa: ‘Fara koyon mulki da baki, kafin ka fara koyo da hannu’ ba. Shi ya sa kalaman sa irin na ɗibgaggun mutane, duk lokacin da ya tashi sai ya feso su kan Kwankwaso domin ci masa zarafi, tare da ƙoƙarin zurfafa gaba a Kano.
NUJ ta Kano ta sami sabbin Shugabanni, sun yi alkawarin kare hakkin ‘yan jarida
A yau ko yaro na goye ya san Doguwa ne gogarman da ya zama kandagarkin hana Kano samun zaman lafiya. Za ta yiwu dama tun ranar gini, to ranar zane, wataƙila bai samu kyakkyawar tarbiyya daga gida ba. Don haka akwai buƙatar a zaunar da shi a koya masa ɗa’a, sanin ya-kamata da mutunta na gaba.
A irin bulkarar da Alhassan ya saba, ya yi ƙoƙarin ganin ya jawo ni ya damalmala cikin irin kwatamin dagwalon ƙazamar siyasar da ya saba wanka a ciki, amma bai yi nasara ba.
Kasagin, wai don ya ɓata min suna, sai ya kawo wata rigima can da ta taɓa faruwa a mazaɓa ta, cikin 2019. To ni dai ina tutiya da kuma alfahari cewa ba a taɓa jin suna na a cikin jangwangwamar tayar da hargitsi ko zargin kisa ba. Kuma ba a taɓa jin baki na ya feso wutar haddasa ƙiyayya da raba kawuna ba. Ni a kullum furuci na shi ne zaman lafiya da kwanciyar hankalin jama’ar mu.
Kuma rikicin da Doguwa ke magana ba wani sharri ba ne wani ya ƙulla. Faɗa ne na ba zato tsakanin magoya bayan wannan jam’iyya da waccan. Kuma na nuna dattako da kyakkyawan shugabanci da wakilci da sanin ya-kamata, na ziyarci wasu da aka ji wa rauni ko rashi, na yi masu jaje. Ban zubar da ƙima da mutunci na ina munanan kalamai ko zunduma ashariya ba.
Amma idan aka koma kan abin da ya faru a Mazaɓar Tudun Wada/Doguwa a can ne ƙaƙara za a ga yadda aka tsara tantagaryar tashin hankali da hargitsi a matsayin hanyar cin zaɓe da tsiya ko da tsiya-tsiya. Kuma Doguwa ne gogarma, ɗan sababin da ake zargi wajen kitsa wannan tashin hankali.
Zanga-zanga: Jami’ar SKYLINE ta baiwa Murtala Gwarmai Jakadan Zaman Lafiya
Kai, ni fa kyakkyawan zubin carbin ficen da na yi, kirki na, mutunci na da kyakkyawan wakilcin da nake wa jama’a su ne gishirin nagartar samun nasarori na a siyasa, ba tayar da hargitsi ba, ba surfa ashariya irin na marasa tarbiya ba ko kasassaɓa irin ta marasa kunyar jama’a ba, ba zargin kisa ba, kuma ba raba kawuna ko son kai na wakilcin kai na ba.
Kuma bari na ƙara faɗa. Ban taɓa ƙaryatawa ko ɓoye kusanci na da Shugaban Ƙasa ba. Ina ɗaya daga cikin Manajojin kamfen ɗin sa na farko, tun kafin na dawo na sake haɗewa da ubangida na a siyasa, kuma mutumin da ya taimake ni wato Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso. Ba ni kaɗai ya taimaka ba. Muna da yawa harda shi Alasan Doguwa.
Ba zan iya saurarawa ko gajiyawa daga kare ƙima, daraja da mutuncin Kwankwaso, Abba da gwamnatin Kano ba, musamman daga cin zarafin da ‘yan-ta-kife irin Doguwa ke yi.
Zaman lafiyar al’ummar Kano fa shi ne zaman lafiyar ƙasar nan. Domin idan aka taɓa hanci, tilas idanu su zubar da hawaye. Na yi amanna cewa mutane irin su Doguwa su ne tantiran waɗanda ba su ƙaunar jam’iyyar su, kuma babu ƙaunar Shugaban Ƙasa a zuciyar sa, saboda irin munanan kalaman da yake furtawa masu ƙara tsananin ƙiyayya da raba kawuna a Jihar Kano, jihar da kusan kamar a kan tsinin mashi take a yanzu.
Sa Hannu:
Sani Ibrahim Paki
Hadimin Yaɗa Labarai,
Ofishin Honorabul Abdulmunin Jibrin
10 ga Agusta, 2024