Daga Kamal Yahaya Zakaria
Mai martaba Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II, a ranar Laraba ya koka da barna tare da wawashe dukiyoyin al’umma da aka yi yayin zanga-zangar da tsadar rayuwa a jihar.
” Kafin faruwar wannan lamarin an sanar da jami’an tsaro cewa akwai yiwuwar bata gari zasu farwa wasu daga cikin Kaddarorin gwamnati da na yan kasuwa amma suka ki daukar matakan da suka dace”
Daily trust ta rawaito sarki Sanusi ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ziyarci madaba’ar jihar Kano da NCC Digital Industrial Park da kuma Shagunan Barakat wadanda ke cikin kadarorin da na masu zanga-zangar suka lalata .

Ya zargi jami’an tsaro da yin sakaci da labarin faruwar lamarin da aka ba su tun kafin faruwar lamarin .
” Kowa yayi da kyau kansa kuma ko ya yi akasin hakan Kansa, muna addu’ar Allah ya baiwa gwamnati ikon gyara Wuraren da aka lalata”.
Ya ce kakansa ya yi aiki da kamfanin buga takardun na Kano inda ya kara da cewa “abin bakin ciki ne yadda jikokinsu suka lalata irin wannan wuri”.
Matasa sun kwashe shinkafa a tsohon gidan wani jami’in gwamnatin Kano
A cewarsa, “Kamar yadda muka saba cewa duk wanda ke da hannu a cikin wannan mugun aikin makiyi ne ga al’ummar Kano .
“Kakana ya yi aiki a nan (kamfanin buga littattafai na Kano). Abin bakin ciki ne yadda jikokinsu suka lalata irin wannan wuri.
“Kafin hakan ya faru, an sanar da jami’an tsaro a rubuce cewa hakan zai faru amma maimakon a hana hakan, sai aka bari hakan ya faru”, in ji shi.
An kafa kamfanin buga littattafai na Kano a shekarar 1938, kuma tun a wancan lokaci take aiki .