Zanga-zanga:APCn Kano ta mayar da zazzafan martani ga kalaman gwamna Abba Kabir

Date:

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas ya ce rashin iya mulki ne yasa gwaman kano a koda yaushe ya ke dora alhakin gazawarsa ga yan adawa .

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a daren jiya ya zargi wasu yan jam’iyyar APCn kano da ingiza masu zanga-zangar da suke rika fasawa da sace kayan gwamnati da na al’umma a Kano.

Talla
Talla

Abdullahi Abbas ya bayyana hakan ne cikin wani sakon murya da aka turowa Kadaura24 a yau Juma’a.

” Duk abun da ya faru sai ya ce mu ne, na fahimci kamar har yanzu ya kasa gane cewa shi yanzu mai mulki ne ba dan adawa ba, duk wata gazawarsa a matsayinsa na gwamna sai ya ce yan adawa ne”.

Shugaban jam’iyyar na APC ya ce ba wani dan jam’iyyar APC da yake da ruwa a abubunwan da suka faru a jihar, Inda ya ce gwamnan ne ya kirawo ruwa kuma ruwan ya kare akansa.

Dalilan ƙazancewar zanga-zanga a arewa

” Kowa yasan yadda malamai su kai ta fadawa al’umma illar yin zanga-zanga har ma suka ce haramun ce a Addinin Musulunci, Amma ranar laraba gwamnan kowa ya ji shi inda ya ke cewa a fito ayi zanga-zangar kuma shi zai fito ya karbe su, to shi ne suma matasan suka ga tunda an gayyace su bari su je su ci irin ganimar da yake ci “. Inji Abbas

Ya kara da cewa suna da labarin yadda wasu jami’an gwamnatin jihar kano suka yi taro da mafarauta kusan rukunonin 70, ” ka je ka bincika ko kasa yan sanda su bincika Maka, in kuma baka da labari to mu mun san Sanda aka yi da inda aka yi da kuma wadanda suka yi”.

Abdullahi Abbas ya kuma shawarci gwamnan da ya mai da hankali wajen yiwa al’ummar jihar Kano aiki kafin lokaci ya kure masa, maimakon daura alhakin gazawarsa akan yan adawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...