Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Daga jiya alhamis da aka fara gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a duk fadin Nigeria ya zuwa yanzu an sanya dokar hana fita a jihohin Arewa guda biyar.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa al’ummar Nigeria sun bayyana cewa za su fara zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a ranar 1 ga watan Ugusta zuwa 10 ga watan.
Tun daga lokaci da aka fara shirya waccan zanga-zanga ne gwamnatin tarayya ta fara fitar da matakai wadanda ta ce zasu taimaka wajen magance matsalar yunwa fatara da dai sauransu dake damun al’ummar Nigeria, tun bayan cire tallafin man fetur.

A jiya alhamis da aka fara Zanga-zangar an farata ne a matsayin ta lumana, amma daga bisani sai ta rikide ta koma ta tashin hankali, bata gari suka shiga cikin yan zanga-zanga suka fara fasa kayan gwamnati da fasa shugunan mutane tare da sace musu kaya.
Misali irin wanna ta Faru a Kano Inda bata garin suka rika fasa shugunan suna dibar Shinkafa, man girki, taliya da dai sauransu.
Tinubu ya Magantu Kan zanga-zangar Jiya Alhamis
Hakan lamarin ya faru a jihar Kaduna da katsina da Yobe, Neja da jigawa, Inda aka rika Kone Kaddarorin gwamnati da na dai-dai kun al’umma.
Wannan dalilin ne ya sanya gwamnonin jihohin suka sanya dokar hana fita a jihohin domin takaita barnar da matasa suka rika yi.
Iftila’i: Yadda masu zanga-zanga a Daura su ka yi yunkurin kutsawa gidan Buhari
Yanzu haka an sanya dokar hana fita a jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Yobe da Borno.
Sai dai lamarin jihar Borno ya banbanta da na sauran, domin a jihar an sanya dokar ne saboda harin kunar bakin wake da aka kai cikin wata kasuwa a kauyen kauri.
Rahotanni da kadaura24 ta sa mu sun nuna cewa a jihohin Arewacin Nigeria ne kadai aka sami tashin hankali a sakamakon zanga-zangar.
Yanzu haka babu jiha ko daya daga kudancin Nigeria da aka sanya dokar hana fita, me yasa hakan ta faru a jihohin Arewa?.