Yanzu-yanzu: An sa dokar hana fita a jihar Borno

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Rundunar ‘yan sanda ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a jihar Borno bayan an kashe mutane 16 tare da jikkata wasu 20 a wani harin kunar bakin wake.

Harin ya faru ne a kauyen Kauri dake karamar hukumar Konduga a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Nahum Daso, a wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri, ya ce an kafa dokar hana fita ne biyo bayan harin bam da ya hallaka wasu mutane da dama da ba su ji ba ba su gani ba.

Talla
Talla

Nahum ya ce matakin ya biyo bayan shawarwarin da Gwamna Babagana Zulum ya yi da shugabannin hukumomin tsaro a jihar kuma an dauki matakin ne domin dakile ci gaba da tabarbarewar tsaro a jihar.

“Wannan dokar hana fita wani mataki ne na hana ci gaba da asarar rayuka da dukiyoyi, da kuma baiwa jami’an tsaro damar inganta tsaro a jihar.

Zanga-zanga: Kwamitin zaman lafiya na Kano ya gargaɗi tubabbun yan daba

“An shawarci mazauna jihar da su kasance a gida kuma su guji yin zirga-zirga a lokacin dokar hana fitar,” in ji shi.

Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu da bin doka da oda, yana mai ba su tabbacin cewa za a ci gaba da sanar da su halin da ake ciki.

Kamfanin dillancin labarai na Nigeria NAN ya ruwaito cewa wani dan kunar bakin wake da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne ya tayar da bam a wata kasuwa da ke garin Kauri, wani kauye a yankin Konduga a jihar Borno.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...