Sarki Kano na 15 ya yi alkawarin isa da koken masu zanga-zanga a Kano ga Tinubu

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, ya tabbatarwa da masu tattaki da sukaje fadarsa cewa zai isar da sakonsu zuwa ga dukkan shugabanni domin tabbatar da cewa an biya dukkan bukatunsu.

Sarkin ya bayyana Hakan ne lokacin da masu yin Tattaki (zanga zanga) sukaje fadarsa dake gidan Sarki na Nasarawa a birnin Kano domin mika masa korafe korafensu akan yanayin halin matsi da tsadar rayuwa da ake ciki a fadin Najeriya

Talla
Talla

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa yana sane da irin yanayin da Kasarnan da kuma al’umar Kasar ke ciki, amma yace babu shakka Addua’a itace maganin wannan al’amari.

A sanarwar da sakataren yada labaran sarkin Abubakar Balarabe kofar Na’isa ya aikowa kadaura24, yace sarkin ya ce “A don hakane ya bukaci al’uma su cigaba dayin addu’oi domin samun zaman lafiya a Kano da Najeriya baki daya”.

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Kano ta saka dokar hana fita ta awanni 24

Kazalika ya godewa masu yin tattakin bisa yadda suka kasance cikin ladabi da da’a ba tareda yin tashin hankali a kan hanya ba, yace al’umar jihar Kano daman al’uma ce mai son zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Alhaji Aminu Ado Bayero sai ya tabbatarwa da al’uma cewa zai mika dukkan kokensu zuwa ga shugaban kasa da dukkan wanda ya dace a Kai masa, tareda cewa an aiwatar da abunda suke bukata domin samun saukin wahalhalun rayuwar da ake fama a yanzu.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace idan za’a iya tunawa dama yasha kiraye kiraye a duk lokacin da al’uma suka kawo masa kukansu a kan wannan hali da ake ciki na matsin rayuwa cewa Gwamnati ta duba kuma ta kawo hanyoyin da al’uma zasu samu sassauci.

A don haka ya sake jaddaawa al’umar cewa zayyi magana da dukkan wani shugaba wanda zai saurareshi domin jaddada bukatar al’uma akan yadda za’a samar da sassaucin matsin rayuwa da ake ciki.

Zanga-zanga: Kwamitin zaman lafiya na Kano ya gargaɗi tubabbun yan daba

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya sake jaddada soyayyarsa da kauna a tsakaninsa da al’umar jihar Kano, tareda bukatarsu su cigaba da kasancewa masu kaunar zaman lafiya da kaunar juna dayin addu’oi a koda yaushe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...