Daga Rahama Umar Kwaru
Wasu fusatattun masu zanga-zanga sun yi dafifi zuwa gidan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke Daura, mahaifar sa a jihar Katsina a ranar Alhamis.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa a yau alhamis ne aka fara zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a duk fadin Nigeria.
Sai dai Zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali a wasu jihohin, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane tare da tilastawa akalla gwamnoni uku kafa dokar hana fita a jihohin.

‘Yan zanga-zangar da suka yi yunkurin kutsawa gidan tsohon dan kasar Nigeria, sun ce sun kosa da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Wani ganau ya shaida wa Daily Trust ta wayar tarho a ranar Alhamis cewa, “Masu zanga-zangar sun cinna wuta a kofar gidan tsohon shugaban kasar kuma suna ta rera waka da karfi.”
A cikin wani faifan bidiyo da Daily Trust ta gani, an ga matasa suna ta ihun, “Bama yi! Bama yi! Bama yi!,”
Sai da wani da ba a san ko wanene ba ya fito daga gidan Buharin, inda ya yi jawabi ga fusatattun matasa.
Yanzu-yanzu: Gwamnatin Kano ta saka dokar hana fita ta awanni 24
Mutumin, a cewar wanda lamarin ya faru a idonsa, ya bukaci masu zanga-zangar da su zabi mutum daya da zai yi jawabi a madadinsu, yayin da aka nade lokacin da ya ke jawabin, kuma aka nuna Buhari bidiyon matashin.
Bayan haka, an ce fusatattun matasan sun nufi fadar Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar Farouk.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun harbi daya daga cikin su a kafa, a kokarin tarwatsa su amma masu zanga-zangar su ka ki ja da baya.
Daily Trust ta rawaito cewa, an tsaurara matakan tsaro a garin Daura sakamakon faruwar lamarin