Daga Isa Ahmad Getso
Tsohon dan takarar gwamnan jihar kano a jam’iyyar PDP Alhaji Jafar Sani Bello ya rubuta takardar koke game da yunkurin sayar da harabar hukumar koyawa matasa sana’o’i ta kasa ITF dake jihar kano.
A wasikar da jaridar kadaura24 ta gani mai dauke da kwanan watan 29, ga watan Yuli 2024, Jafar Sani Bello yace ya sami bayanai da suke nuna cewa ana shirin sayar da harabar hukumar wacce aka samar don cigaban jihar kano da al’ummarta.

” Na damu sosai dana sa mu sami labarin jami’an hukumar ku ta ITF sun hada kai da wasu masu harkar filaye suna kokarin sayar da harabar hukumar, wanda hakan ba daidai ba ne”.
Da dumi-dumi: Tinubu ya rage farashin Shinkafa a Nigeria
Ya ce sayar da harabar hukumar ta ITF zai kawo cikas ga aiyukan hukumar na ba da horo ga matasa don su dogara da kawunansu .
Jafar Sani Bello ya ce yana fatan hukumar ta ITF ta kasa da ta dakatar da kudirinta na sayar da harabar hukumar da gwamnatin jihar kano ta bata don koyawa matasan jihar sana’o’i .

Ya ce sayar da harabar hukumar zai cutar da jihar Kano da matasan jihar, domin aikin da aka samar da hukumar don shi zai kadata ko ya sami tasgaro.