Daga Rukayya Abdullahi Maida
Al’ummar Arewaci da kudancin Nigeria sun harzuka bayan da mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara, akan ta su suka rika kai kararsa fegin Facebook wanda hakan yasa suka rufe shafin nasa.
Mawakin ya saki waƙar Inda yake nuna godiya ga shugaban kasa kan halin da ake ciki musamman kan matakin da ya dauka na dawo wa da kananan hukumomi yancin cin gashin kansu.
Wakar dai ta jawo chache-kuce tun daga jiya juma’a zuwa yau asabar musamman a dandalin Facebook, X da Intergram da TikTok.
Gwamnatin Nigeria ta fara yunkurin sassanta Ɗangote da hukumomin man fetur na kasar
Yanzu haka dai bayan cika ka’idoji dandalin Facebook sun rufe shafin nasa mai suna “Dauda Kahutu Rarara”.
Yanzu Kuma matasan sun dukufa kai karar Dauda Kahutu Rarara ta neman a rufe shafukansa na Intergram da TikTok.
Ga hotunan yadda aka rufe shafin na mawaki Rarara.